“Na Haɗa Kayana Na Bar Gidan": Wani Magidanci Yayi Fushi Ya Bar Matarsa Bayan Da Surukarsa Ta Dawo Gidansu

“Na Haɗa Kayana Na Bar Gidan": Wani Magidanci Yayi Fushi Ya Bar Matarsa Bayan Da Surukarsa Ta Dawo Gidansu

  • Wani magidanci ya bayar da labarin yadda ya rasa aikinsa, sannan kuma yanayin mu'amalarsa da iyalinsa ta canza saboda rashin kuɗi
  • Bayan rasa aikin nasa, matarsa ta ci-gaba da ɗaukar nauyin ciyar da gidan baki ɗaya saboda ta na samun kuɗi fiye da mijin
  • Sai dai sun fara samun matsala ne tun bayan lokacin da surukarsa ta dawo gidan nasu, wanda hakan ya yi sanadin barinsa gidan

Wani magidanci ya bayyana yadda ya bar matarsa bayan rasa aikinsa na banki da ya yi sanadiyar jefa shi cikin halin ƙarancin abin hannu.

Labarin wanda @Ekwulu ya wallafa a shafinsa na Tuwiter, mutumin ya ce ɗabi'iun matarsa sun sauya daga lokacin da ta fara ciyar da gidan nasu.

Mata da miji
Magidanci Yayi Fushi Ya Bar Matarsa Bayan Da Surukarsa Ta Dawo Gidansu. Hoto: Getty Images/valentinrussanov and JGI/Jamie Grill
Asali: Getty Images

Matar ta sauya daga yadda take a da

Bayan ya rasa aikinsa kuma ya kasa ɗaukar ɗawainiyar gidan, sai matarsa ta karɓi ragamar ciyar da su saboda tana samun kuɗaɗe fiye da mijin na ta.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ya yi mamaki a lokacin da ‘yan uwan matarsa su uku suka dawo gidansu da ke Lekki a jihar Legas da zama.

Bayan nan sai ita ma surukarsa ta dawo gidan nasu, hakan ya sa ya ji ya ƙara takura sosai.

Ya bar gidan kowa ma ya huta

Ga abinda wani ɓangare na rubutun ya ke cewa:

"Matata ke biyan kuɗin haya, kuɗin makarantar yara da dai sauransu, abin ya ƙara munana lokacin da aka ƙarawa matata girma. Sai kuma surukata ta dawo gidan, wata rana da yamma ta shigo ɗakin cin abinci ta goranta min wai abinci ne kawai nake son ci ko da yaushe.
"Na faɗa mata ta daina shiga cikin rayuwar aurena, anan ne har muka yi musayar yawu. In taƙaice muku bayani, matata ta dawo ta tarar damu, daga nan ta fara masifa kan cewa na zagi mahaifiyarta. Gari na wayewa, na haɗa kaya na na ƙara gaba."

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Wata Mata Ta Rasa Ranta a Kokarin Raba 'Ya'yanta Fada a Birnin Tarayya Abuja

Matar ta rasa aikinta bayan shekara guda

Mutumin ya ce ya bar duk wani abu da ya mallaka a gidan, daga bisani kuma ya sha fafutuka har zuwa lokacin da ya samu wani aikin mai kyau, sannan komai ya dawo daidai.

Ya ce yanzu zai iya biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansa da kula da su amma ya sha alwashin ba zai sasanta da matarsa ba.

Ita ma matar ta rasa aikinta, ta yi ƙoƙarin yin sulhu da shi, amma ya ƙi yarda da hakan..

Ga dai labarin, da kuma yanayin martanin da mutane suka yi a ƙasa:

Miji ya ɗirkawa matarsa ciki bayan yunƙurin rabuwarsu

A wani labarin namu na baya, kun ji yadda wani mutum ya yi wa matarsa ciki bayan yunƙurin rabuwar da suka yi.

An bayyana cewa matar da mijin sun gama yanke shawarar cewa za su rabu kowa ya kama gabansa a lokacin da abin ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng