Dan Najeriya Yemi Mobolade Ya Lallasa Abokin Takararsa, a Zaɓen Magajin Garin Colorado Springs na Amurka

Dan Najeriya Yemi Mobolade Ya Lallasa Abokin Takararsa, a Zaɓen Magajin Garin Colorado Springs na Amurka

  • Wani ɗan Najeriya mai suna Yemi Mobolade ya zama magajin garin Colorado Springs na ƙasar Amurka bayan samun nasara kan abokin hamayyarsa
  • Yemi ya samu kaso 57% na kuri’un da aka kaɗa, yayin da abokin gwabzawarsa na jam’iyyar Republican Wayne Williams, ya samu kaso 43% na kuri’un
  • Yemi, wanda ya koma da zaman Amurka a shekarar 2010, zai kasance baƙar fata na farko da ya taɓa zama magajin garin, lamarin da aka bayyana da girgizar siyasa kasar

Colorado, kasar Amurka - An zaɓi wani ɗan Najeriya a matsayin magajin garin Colorado Springs da ke ƙasar Amurka.

An ayyana mutumin mai suna Yemi Mobolade a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun kaso 57% na ƙuri’un da aka kaɗa, inda ya yi nasara kan abokin hamayyarsa na jam’iyyar Republican Wayne Williams.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka Ta Yi Martani Kan Harin Da Aka Kai Kan Jami'anta a Jihar Anambra

Wayne Williams, wanda tuni ya amshi shan kaye sannan kuma ya taya Yemi murna, ya samu kaso 43% ne na kuri'un da aka kaɗa.

Mobolade
Dan Najeriya Yemi Mobolade Ya Lashe Zaɓen Magajin Garin Colorado Springs na Amurka. Hoto: yemiformayor.com
Asali: UGC

Ya koma Amurka a 2010

Yemi, wanda ya koma da zaman Amurka a shekarar 2010, na gudanar da kasuwancinsa ne a cikin birnin na Colorado, kuma wannan nasara da ya samu, an bayyana ta a matsayin girgizar siyasar ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yemi Mobolade ɗan takara ne da ke cin gashin kansa a siyasance, a haka kuma ya yi takarar har ya yi nasara.

Jawabinsa na neman zabe

Ya bayyana a shafinsa na yaƙin neman zaɓe cewa:

"Ni ɗan siyasa ne mai zaman kansa, kuma gogagge a wajen haɗa al'ummomi mabanbanta, gami da haɗa kawunan jama'a kan manufa guda.
"Na samu nasarar ɗaga wasu mazauna birnin nan, ƙananan 'yan kasuwa, da ma manyan 'yan kasuwa zuwa matakin kafuwar arziki, haka nan kuma na zo da sabbin hanyoyin da za su sa garinmu ya yi wa kowa da kowa daɗin zama”

Kara karanta wannan

Bautar Ƙasa: Bai Kamata Shirin NYSC Ya Zama Wajibi Ba, Farfesa Jega

Ya yi alƙawarin yin shugabancin da za a yaba

Ya bayyana cewa zai jagoranci mutanen yadda ya kamata, zai sharewa mutanen da ba su gamsu da yanayin shugabancin da ke gudana a yankin ba hawaye.

Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe, cikin murna Yemi ya bayyana cewa birnin Colorado Springs zai zama birni mai tarin al'adu, da kuma tattalin arziki.

Jaridar Colorado Sun ta ruwaito cewa Yemi zai kasance baƙar fata na farko da zai riƙe muƙamin magajin gari a Colorado Springs.

Amurka ta yi martani kan harin da aka kai wa ma'aikatan ta a Najeriya

A wani labarin da muka wallafa a baya, kun ji cewa ƙasar Amurka ta yi magana kan harin da aka kai wa ma'aikatan ta a jihar Anambra.

An dai kai harin ne jiya Talata da yamma a ofishin jakadancin Amurka da ke ƙaramar hukumar Ogbara ta jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng