“Yanzu Ba Na Son Mijina": Cewar Wata Mata Yar Najeriya Da Mijinta Ya Ɗauki Nauyin Karatunta Zuwa Birtaniya

“Yanzu Ba Na Son Mijina": Cewar Wata Mata Yar Najeriya Da Mijinta Ya Ɗauki Nauyin Karatunta Zuwa Birtaniya

  • Wata ma'aikaciyar jinya ta nemi shawarar masu amfani da kafafen intanet dangane da yadda ta ji ta daina son mijinta
  • Ta ce babu gaira babu dalili ta ji ta daina sonsa duk da shi ya ɗauki nauyin karatunta zuwa Birtaniya da ya ke da zama
  • Ta ce mijin ya magance ma ta matsalolinta da na 'yan uwanta a lokacin da suke a Najeriya, sannan shine ya yi mata ƙoƙarin barin ƙasa

Auren wasu 'yan Najeriya mazauna ƙasar waje na fuskantar ƙalubale biyo bayan bayanin da matar ta yi na cewar ba ta sha'awar auren yanzu.

Wata mai suna Anthonia Ogbewe ce ta wallafa labarin a shafinta na TikTok in da ta bayyana cewa matar na da shekaru 28 a yayin da mijin kuma ya ke da shekaru 32.

Kara karanta wannan

"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Zata Koma Kasarsu

Yar Najeriya/Birtaniya/Rikicin Ma'aurata
Ta ce yanzu ta dena son mijinta. Hoto: Atstock Productions, Lighthouse Films
Asali: Getty Images

Mijina ne ya sanya na karanci aikin jinya

Matar ta ce mijin nata ne ya ce ta karanci ilmin jinya a sa'ilin da ta ke a Najeriya kuma shine ya riƙa taimaka ma ta wajen ɗaukar nauyin karatun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matar ta kuma ƙara da cewar ya biya ma ta buƙatunta da dama hadda ma wasu daga cikin ɓuƙatun 'yan uwanta, sannan kuma shine ya ɗauki nauyin takardun tafiyarta zuwa ƙasar waje.

Ta ce ta faɗa masa cewa ita fa ba ta ra'ayin auren na su, amma kuma sai ya ke tunanin ko domin kawo ta ƙasar Turai da ya yi ne, kuma ya ke faɗawa mutane hakan.

Ban san dalilin da ya sa na daina sonsa ba

Daga ƙarshe ta ce ba ta san dalilin da ya sanya ta daina son mijin na ta ba, kuma ba ta son ci gaba da zama a auren da babu soyayya a ciki. Matar ta nemi mutane su ba ta shawara kan hakan.

Kara karanta wannan

Mutuwar Aure: Maimunatu Giwa Ta Ce Ko Jibganta Miji Ke Yi Ba Za Ta Bar Shi Ba

Kalli bidyon daga ƙasa

Ra'ayoyin da jama'a suka bayyana:

Mathewl23 ya ce:

“ki yi ƙoƙarin tuno rayuwar da kuka faro tare a baya.”
“Daga nan za ki iya cimma matsaya ki ba wa kan ƙi amsa, amma dai abinda Ubangiji ya yi shine ya fi ba wai zaɓin ki ba.”

kohl ya ce:

“Ina mai shawartar ki da ki je hutun sati biyu a wani yanki na kudancin Amurka, ina mai tabbatar miki da cewar soyayyar za ta dawo.”

RePøßt ya ce:

“Hidimar iyali akwai wahala. Ina ganin rayuwarki ce, kuma za ki iya gudanar da ita yadda ki ka ga dama, fatan dai kar ki yi da na sani a gaba.”

Pau G kuma cewa ya yi:

“Kawai ki biya shi kuɗaɗen da ya kashe hadda ƙari ma, ki maida masa kuɗaɗen da ya kashe miki, daga nan sai ki dawo Najeriya.”

Frank Izoukumor kuma ya ce:

Kara karanta wannan

"Na Tuba Ba Zan Kara Ba", Matashi Ya Koka Bayan Ya Sanya N400k Na Mahaifiyarsa a Caca, Sun Bace Bat

“Abin fa mai sauƙi ne, kawai dai ki ce kin ga wani da ya fi shi kyau, shine za ki zo ki na faɗin cewa kin daina son mutumin da ya yi ɗawainiya da ke."

Wata budurwa ta rabu da saurayinta bayan ya kaita ƙasar waje

A kwanakin baya ma sai da muka wallafa labarin wata budurwa da ta rabu da saurayinta bayan ya kaita ƙasar waje.

Wani mai amfani da shafin Tuwita mai suna @akunesiobike12 ne ya wallafa labarin da ya ce ya faru ne da abokinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng