Shiri Ya Kwabe: Bayan Mutuwar Matar Sa, Magidanci Ya Yi Gwajin DNA, Ya Gano An Caka Masa 'Ya'ya

Shiri Ya Kwabe: Bayan Mutuwar Matar Sa, Magidanci Ya Yi Gwajin DNA, Ya Gano An Caka Masa 'Ya'ya

  • Wani magidanci ya gano cewa yara biyun da ya ke riƙe da su har na shekara 2 a matsayin ƴaƴan sa, ba nasa ba ne
  • Magidancin ya gano hakan ne bayan ya yanke shawarar zuwa yin gwajin DNA domin gano ko shine ainihin mahaifin ƴaƴan na sa
  • Abin takaicin shine, bayan mutuwar matar sa, abin ya zama da matuƙar wahala ya iya gano haƙiƙanin mahaifin yaran

Wani magidanci da ya je yin gwajin DNA, ya gano cewa yaran da ya ke riƙe da su a hannun sa, ba ƴaƴan sa ba ne.

Magidancin mai shekara 36 a duniya ya bayyana cewa sun haifi ƴaƴa biyu tare da matar sa wacce yanzu ta mutu.

Magidanci ya gano 'ya'yan sa 2 ba na shi ba ne
Bayan yin gwajin DNA ya gano 'ya'yan ba na shi ba ne Hoto: Getty Images/Petri Oeschger da @jon-d-doe. Hoton farko sanya wa kawai aka yi
Asali: UGC

Abin takaicin shine, mutuwar matar sa ya zama babban ƙalubale a gare shi wajen gano haƙiƙanin mahaifin yaran.

Kara karanta wannan

“Kai Kuwa Ka More”: Wani Matashi Ya Ɗora Bidiyon Mahaifinsu Na Musu Rabon Gado

Bayan mutuwar matar ta sa ne dai ya yanke shawarar zuwa yin gwajin DNA, inda sakamakon da ya samu ya girgiza shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin wanda ya rasa abin yi dangane da lamarin, ya garzaya manhajar Facebook, inda ya ke neman shawara daga wajen mutane.

Rubutun da aka yi a Facebook, ya samu isa manhajar Twitter, inda wani mai amfani da sunan jon_d_doe @, ya sake wallafa shi.

Mutane da dama sun ba shi shawarar abinda yakamata ya yi.

Ga kaɗan daga ciki:

@The_HSE_Officer ya rubuta:

"Abinda ya fi masa shine ya mayar da yaran ga iyayen matar sa da ta mutu, ya cigaba da rayuwar sa kawai. Idan har mahaifin yaran nan gaba ya zo karɓar abin sa, baya da wata asara."

@NGBBTrippleKing ya rubuta:

"Ina tunanin wannan shine abu mafi muni da ka iya aukuwa ga wani mutum."

Kara karanta wannan

"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari

@7Inches_LONG ya rubuta:

"Kam sirrin da mata da yawa su ke tafiya da shi zuwa kabari ba ƙarami ba ne."

@kelex213j ya rubuta:

"Kwata-kwata wannan ba adalci ba ne."

@TenaLion007 ya rubuta:

"Ka ɗauko wayar ta. Ka duba dukkanin saƙonnin ta da lambobin da ke ciki, tabbas za ka gano mahaifin ko mahaifan yaran."

Budurwa Ta Ba da Labarin Yadda Ta Kare Bayan Ziyartar Saurayinta

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta bayyana yadda ta kaya tsakanin ta da saurayin ta, bayan ta kai masa ziyara.

Budurwar ta gano cewa ashe maƙoƙo ne domin ko taro ya hana ta lokacin da ta zo tafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng