Mahaifiyar Wani Dan Najeriya Da Ke Kasar Waje Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa Bayan Cinye Kudin Da Ya Ke Aiko Mata

Mahaifiyar Wani Dan Najeriya Da Ke Kasar Waje Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa Bayan Cinye Kudin Da Ya Ke Aiko Mata

  • Wani dan Najeriya na aiko da kudi daga kasar waje ga mahaifiyarsa, da nufin ta tara masa
  • Bayan dawowarsa gida a yankin Kudu maso gabas ya tarar ta cinye komai, ya dawo ba shi da ko sisi
  • Labarin ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta yayin da mutane ke alakanta shi da labarin Achraf Hakimi

Wani dan Najeriya mai suna Napaul ya shawarci mutane da su dinga addu'ar neman dace wa a komai saboda ba lallai abin da ya yi aiki ga Achraf Hakima ya yi aiki gare su ba.

Naupal ya yi wannan jawabin ne a shafinsa na Tuwita lokacin da ya ke bada labarin irin takaicin da wani mutumin Owerri ya ji bayan mahaifiyarsa ta ci amanarsa.

Saurayi da murya
Hotunan misali na saurayi da mace: Hoto: Favour Nnebedum, Ibrahim Sani
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

An Zarge Shi da Bada Cin Hanci, Dino Melaye Ya Fadi Yadda Ya Samu Takarar Gwamna

A cewar Naupal, ya san wani mutum da ke aiki a kasar waje da ke turo kudin ajiya ga mahaifiyarsa.

Sai dai, mutumin ya dawo gida ya tarar ba kudin da ya rage. Ma'ana dai yanzu ba shi da komai.

Ga abin da Naupal ya wallafa:

"Na san wani mutumin Owerri da ya yi aiki a kasar waje ya ke turo kudi ga babarsa ta ajiye masa, abin dariyar da ya dawo ya tarar ba shi da komai.
"Rayuwar nan ba tabbas.
"Abin da ya yi aiki ga Hakimi ba dole ne ya ma aiki ba, kai dai kayi fatan dacewa a kowanne hali ka tsinci kanka."

Martani a kafar sadarwa

Oparakenneth7 na cewa:

"Idan na bawa mahaifiyata ₦100,000 ajiya. Ko dari biyar ba zata dauka ba a ko shekara 5 za a yi. Ko kudin ajiya da banki ke dauka ba za ta dauka min ba."

Kara karanta wannan

“Ta Gaji Da Auren Tun Ba a Kai Koina ba” Bidiyon Amarya Tana Kicin-Kicin Da Rai Yayin da Take Jerawa Da Angonta Ya Yadu

Cewar David22042527:

"Ya faru ga dan kanin babata. Ya shafe shekaru a Dubai yana neman kudi yana turowa babarsa ta ajiye. Abin takaici da ya dawo Najeriya, babarsa ta cinye miliyoyin kudaden. Ya dawo ba ko sisi."

In ji @jubilant101

"Abin da ya ma wani aiki, bai zama lallai yayi wa wani ba. "Mafita shi ne, kasan nagartar makusantanka ka kuma san yadda zaka yi mu'amala da kowa."

@534_angeli na cewa:

"Duk da haka sai na turawa babata ₦5000 din ta rage min a Palmpay ta ajiye min da sunanta...ba abin da ya dame ni."

In ji @MickyLaz:

"Idan kana da matsala da mahaifiyarka ka je a sasanta, kada ka dame mu a nan. "Saboda yadda ku ke surutu tun bayan fitar labarin nan ni ban gane ba."

Cewar @WhyKayJr:

"Ya na faruwa fa saboda mun yi haka da mahaifina, lokacin da nake gini ina makaranta ban cika zuwa wajen aikin ba, sau biyu ina biyan kudin bohal, kuma ba a yi ba, har sai da na dawo na yi da kudina."

Kara karanta wannan

“Suna Rayuwa Kamar Tagwaye” Matashi Ya Yada Bidiyon Kyawawan Matansa 2 Sanye Da Kaya Iri Guda

Amarya ta murtuke fuska a bidiyo yayin da ta ke jera wa tare da angonta

A wani lamari mai da ya kamata ya zama abin farin ciki, an gano wata amarya ta murtuke fuska a ranar aurenta.

Galibin dai amare an saba ganinsu suna cikin annashuwa da farin ciki a ranar aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164