Bidiyon Wani Malamin Addini Na Huduba Cikin Harshen Igbo Ya Yadu Sosai
- Wani bidiyon malamin addinin musulunci yana huɗuba cikin harshen Igbo a wani masallaci a birnin Abuja ya janyo musayar ra'ayi
- Malamin addinin ya gudanar da huɗubar sa ga mutanen da suke zaune cikin masallacin cikin natsuwa
- Wannan dai abin mamaki ne sosai saboda sanin cewa ba a cika samun Musulmai ba a cikin ƴan ƙabilar Igbo
Wani bidiyo ya nuna wani malami wanda ya fito daga yankin Kudu maso Gabas na Najeriya yana huɗuba cikin harshen Igbo a cikin wani masallaci a birnin tarayya Abuja.
A cikin bidiyon wanda ya karaɗe yanar gizo an nuna malamin yana huɗuba ga ɗumbin mutanen da suka zo masallacin domin sauraron huɗubar da niyyar samun lada da ƙara ƙarfin imanin su.
Malamin yana riƙe da takardar huɗubar sa, lokacin da yake ta ƙwararo huɗubar sa cikin harshen Igbo gwanin ban mamaki.
Mutane da dama da suka yi magana akan bidiyon sun bayyana cewa baƙon abu ne ganin an gudanar da huɗuba a cikin harshen Igbo, wanda hakan ya sanya ta ɗauki hankula.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ya zuwa lokacin da aka buga wannan labarin, sama da mutum ɗubu ɗari biyu da talatin da biyar (235,000) suka kalli bidiyon yayin da sama da mutum dubu ɗaya da ɗari biyar (1500) suka sake wallafa shi.
Mutane sun cika da mamaki
Ga kaɗan daga cikin sharhin da mutane suka yi akan bidiyon:
nkechinweze ya rubuta:
"Awwwww gaskiya wannan yayi kyau! Ashe ba a harshen larabci kawai ake yin huɗuba ba. Na yaba maka ɗan'uwa, shin ana kiran Sallah a harshen Igbo?"
@moh_selis ya rubuta:
"Babu wata ƙabila a duniyar nan da ba za a samu musulmi ba a cikin su, musulunci haske ne wanda waɗanda Allah ya zaɓa kawai suke ganin shi. Tasowa cikin addinin musulunci babbar rahama ce, Alhamdulillah."
@omoakeen ya rubuta:
"Na ji daɗin sanin cewa hakan ya faru, wannan ne karon farko da na ga irin hakan. Sau ɗaya kawai na taɓa ganin Alhaja Ngozi"
Legit Hausa ta zama jin ta bakin wasu mutane kan ko sun taɓa cin karo da karatun wani malami musulunci cikin harshen Igbo, ko sun taɓa haɗuwa da wani musulmi ɗan ƙabilar Igbo.
Da yawa daga cikin su sun bayyana cewa gaskiya ba su taɓa yin ko ɗaya daga cikin biyun ba, dalilin su kuwa shine, sanannen abun ne cewa a ƙabilar Igbo babu yawan musulmai sosai.
Ɗaya daga cikin waɗanda muka samu tuntuɓa mai suna Sahabi ya bayyana cewa gaskiya bai taɓa gani ba amma yana jin labarin cewa akwai musulmai a cikin su.
Wani mai suna Ahmad kuwa bai yi mamaki ba domin a cewar sa ya san cewa ana samun musulmai a cikin ƙabilar Igbo, amma basu da yawa sosai.
Sarkin Saudiyya Ya Tuna da Mutanen Jihar Kano Yayin da Aka Soma Azumin Ramadan
A wani labarin na daban kuma, Saudiyya ta waiwayo kan mutanen jihar Kano a yayin da aka fara gudanar da azumin watan Ramadan.
Ƙasar ta aiko da kayayyakin abinci domin rabawa mutanen jihar.
Asali: Legit.ng