Bidiyon Matashi Mara Hannu Mai Rubuta Da Ƙafa Ya Ɗauki Hankula

Bidiyon Matashi Mara Hannu Mai Rubuta Da Ƙafa Ya Ɗauki Hankula

  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yabawa wani matashi mara hannuwa bisa wata baiwa ta musamman da ya nuna duk da nakasar da yake da ita
  • Matashin mai suna Psammy, ya ba masu amfani da yanar gizo mamaki lokacin da ya koma yana amfani da ƙafafun sa wajen yin WhatsApp
  • Wasu daga ciki sun yi mamakin yadda yake yin rubutun cikin sauri, wasu kuma sun yaba masa inda suke cewa sun yi ƙoƙarin jarabawa amma sun ji ba za su iya ba

Wani bidiyon wani matashi mara hannuwa yana latsa wayar sa da yin WhatsApp ba tare da wani ya taimaka masa ba, ya ɗauki hankula sosai.

A cikin wani bidiyo da aka sanya a TikTok, matashin mai suna Psammy, ya jingina bayan sa jikin bango sannna yayi amfani da wayar sa wacce ya riƙe da ƙafar dama.

Matashi
Bidiyon Matashi Mara Hannu Mai Rubuta Da Ƙafa Ya Ɗauki Hankula Hoto: TikTok/Psammy07
Asali: UGC

Da ƴan yatsun ƙafarsa ya shiga cikin WhatsApp kamar yana amfani da hannuwan sa.

Yayi amfani da wayar cikin sauri ta yadda wanda baya da masaniya kan naƙasun da yake da shi zai ɗauka cewa wannan rubutun da Larabci aka yi shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama sun yaba masa kan yadda yake yiwa rayuwa kyakyawar fahimta.

Ga kaɗan daga ciki:

Tiktok Report ya rubuta:

"Dan Allah kayi bidiyon yadda kake cajin wayar ka."

SGS_OFFICIAL ya rubuta:

"Yana da sauri."

user1958577163103 ya rubuta:

"Alhamudulilah bisa ni'imomin da Allah yai mana a rayuwa. Ina maka fatan ƙara samun ƙarfin guiwa ɗan'uwa."

Balogun2345 ya rubuta:

"Na jaraba yin hakan amma ban ji daɗi ba. Yanzu nasan abinda mara hannu ke ji."

emmiblinks ya rubuta:

"Allah ina roƙon ka yafe min ƙorafe-ƙorafen da nake yi. Ka cigaba da haƙuri ɗan'uwa."

Matashi Mara Hannuwa Ya Zama Tela, Ya Ɗinka Kaya a Cikin Wani Bidiyo

A wani labarin na daban kuma, wani matashi mai gundulmin hannuwa ya zama tela, ya ɗinka kaya cikin ƙwarewa a wani bidiyo.

Matashin dai ya zaɓi da ya tashi ya nemi na kan sa duk kuwa da nakasar da yake fama da ita. Hakan ya sanya ya samu yabo sosai a yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng