Wani hazikin dan Najeriya ya kera mota mai lafiya da N80,000 kacal
- Wani dan Najeriya ya kera motar hawa ba tare da amfani da kayayakin kasashen waje ba
- Mutumin ya kashe jimlar kudi N80,000 katchal wajen kera motar da ke aiki kamar yadda kowace mota keyi
Akwai mutane masu dimbin basira da hazaka a Najeriya. Hakan yasa lokaci zuwa lokaci zaka ka yan Najeriya sun kera wasu abubuwan da zaiyi wuya kayi tsamanin abin zai yiwu da farko.
Da zarar an ambaci kere-kere, abina ke firgita mutane shine zunzurutun kudaden da za'a kashe sai dai lamarin ba haka yake ba musamman idan mutum ya san inda zai samu abubuwa masu araha da zai yi kere-keren nasa.
Francis Emmanuel, wani matashi ne da ke zaune a garin Aba na jihar Abia wanda yayi wani abin mamaki inda ya kera lafiyayar mota da kudi naira 80,000 katchal.
Emmanuel ya sanya wa motar suna EM Emulate ya bayyana cewa yayi amfani da injin babur kirar Mate da kuma sauran karafe da robobi da ya samu a Najeriya wajen kera motar.
KU KARANTA: Ana musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da gwamna Ajimobi
Emmanuel ya ce ya kera mota guda daya ne katchal saboda rashin isasun kudade kuma ya ce a shirye yake yayi aiki tare da duk wani mai niyyar saka jari cikin harkar nasa don bunkasa basirar kerar motocin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng