Jaruma Halima Abubakar Ta Ce A 'Kama' Fitaccen Malamin Addinin Najeriya Idan Wani Abu Ya Faru Da Ita
- Rikicin da ke faruwa tsakanin fitacciyar jaruma, Halima Abubakar da fitaccen malamin addini, Apostle Suleiman ya girmama
- Jarumar ta tafi shafinta na Instagram ta wallafa wani sako mai karfi ga dubban magoya bayanta game da malamin addinin na kirista
- Ta yi alkawarin cewa ba abin da zai faru da ita kuma idan wani abu ya faru su kama Suleiman da laifi
- Kalamanta ya janyo martani masu ban dariya, wasu yan Najeriya suna ta bawa abin fassara daban-daban
Kazamin rikicin da ke tsakanin jaruma, Halima Abubakar, da fitaccen fasto, Apostle Johnson Suleiman ya dauki sabon salo a yayin da jarumar ta yi magana mai karfi game da malamin addinin.
Halima ta tafi shafinta na Instagram domin aika gargadi ga faston tare da sanar da magoya bayanta abin da ke faruwa a yanzu.
Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A rubutun da ta wallafa, jarumar ta bukaci masoyanta kada su damu amma idan wani abu ya faru da ita su kama malamin addinin.
A cewar ta:
"Kada ku tada hankalin ku game da ni. Amma ku rike Johnson Suleiman ko da wani abu ya faru. Ba za ka iya komai ba dai. Yan Najeriya, ku sani. Idan wani abu ya faru Johnson kai ne."
Ga abin da ta wallafa a kasa:
Yan Najeriya sun yi martani kan rubutun da Halima ta wallafa
Masu amfani da dandalin sada zumunta a kasar sun yi martani daban-daban kan rubutun na Halima Abubakar game da rikicin ta da Apostle Suleiman.
Legit.ng ta zabi wasu daga cikinsu:
Marauniquestore:
"Lokacin da ki ke kwanciya da shi ba ki fada mana cewa Johnson ne ba yanzu da abubuwa suka tabarbare johnson ne... don Allah ku kyalle mutane su numfasa."
Sylvia_adun:
"Allah ya tsare ta ya bata damar sauya rayuwanta tunda ta riga ta amsa kurakurenta."
Jackiemartins0679:
"Ba ki ji tsoron kwanciya da malamin addini ba, yanzu abu ya tabarbare, kina fada mana, Halima ki rika jin tsoron Allah faaa."
Jollifellow:
"Malamin wasu ne ake maganansa haka fa ... Allah ya kyauta."
Asali: Legit.ng