Wata Sabuwa: Kotu ta datse igiyoyin aure kan zargin mijin ya faɗa soyayya da kare
- Kotun kwastumare a jihar Legas, ta raba auren wasu ma'aurata bisa zargin mijin ya faɗa soyayya mai ƙarfi da karensa
- Alkalin kotun ya umarci ma'auratan kowa ya tafi harkokinsa na daban, daga yanzu su ba mata da miji bane
- Kazalika ya umarci matar da cigaba da rainon ɗan da suka haifa, shi kuma mijin ya rinka ba ta kuɗin ciyarwa
Lagos - Wata yar kasuwa, Rashidat Ogunniyi, wacce ke tuhumar mijinta da nuna soyayya da kula ga karensa fiye da ita, ta samu abin da take nema a kotu.
Premium Times ta ruwaito cewa wata kotun Kwastumare dake zamanta a jihar Legas, ta datse igiyoyin auren mutanen biyu.
Akalin kotun, mai shari'a Adeniyi Koledoye, ya bayyana cewa rashin halartar wanda ake zargi zuwa kotun ba zai hana cigaba da sauraron Shari'ar ba.
Alkalin ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Tun da aka fara sauraron wannan ƙarar, wanda ake zargi bai girmama zaman kotu ba, saboda haka kotu ba ta da wani zaɓi da wuce ta datse auren baki ɗaya."
"Bisa haka kotu ta na mai sanar da cewa ta raba auren dake tsakanin Mista Kazeem Ogunniyi da mai ɗakinsa Rashidat Ogunniyi, yau. Daga yanzun babu auren miji da mata tsakanin su."
"Kowa ne ɗayan su zai tafiiyar da harkokinsa daban, Kotu na muku fatan Alkairi a harkokin da kuka sanya a gaba."
Shin ma'auratan ba su da 'ya'ya ne?
Game da ɗa guda ɗaya da Allah ya albarkaci ma'auratan da shi, Kotun ta yanke hukuncin barin yaron a hannun matar, kuma ta umarci tsohon mijin ya rinka biyanta N10,000 na ciyarwa duk wata.
Kazalika, Alkalin kotun ya ɗora ɗawainiyar karatun yaro a wuyan Mista Ogunniyi, da sauran harkokin jin daɗi na yaron.
Mijina ya fi kulawa da karensa
Tun da farko Rashidat ta nemi kotu ta raba auren wanda ya shafe shekara 12, inda ta yi ikirarin cewa mijinta ya fi kula da jin daɗin karensa fiye da iyalansa.
Matar tace:
"Kazeem ba shi da kulawa a matsayin miji da kuma uba, baya nuna soyayya gare ni da kuma ɗan da muka haifa. Ya fi kula da lafiya, farin ciki da kuma rayuwar karensa."
A wani labarin na daban kuma Kwastam sun hama Hodar Iblis ta Biliyan N3.9 a wata mota dake ɗakko litattafan Addini
Jami'an hukumar Kwastam dake aiki a Seme da Badagry sun cafke wata motar ɗauko litattafan addini ta ɗauko Hodar Iblis.
Kakakin kwastam, Hussaini Abdullahi, yace jami'an sun gano cewa Hodar ta kai darajar Naira Biliyan N3.9bm.
Asali: Legit.ng