Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

  • Wani mutum mai suna Adam Muhammed ya fara tattaki tun shekarar 2021 daga birnin Landan inda ya bayyana fatansa na zuwa Makka da kafa
  • Mutanen da suka yaba da irin wannan azama tasa sun fito don taimaka masa a hanya da abinci da wurin kwana don cimma burinsa
  • A cewar mai tattakin, zai ratsa ta Jordan da Syria, kuma yana da burin kammala tafiyar tasa a watan Yulin bana

Wani mutum mai shekaru 52, Adam Muhammed, ya yanke shawarar yin tattaki daga birnin Landan zuwa Makka da kafa. Ya fara tafiya a watan Agusta 2021.

Tsawon watanni da fara tafiyar, ya kan rubuta komai da ke tafiya ta yanar gizo, inda mabiyansa suke taya shi murna da kara masa karfin gwiwa.

Kara karanta wannan

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Muhammad Adam mai kudurin zuwa makka da kafa
Mutumin da ya fara tattaki tun 2021 daga Birtaniya ya isa Turkiyya, yana son zuwa Makka a watan Yuli da kafa | Hoto: TRT World
Asali: Instagram

Mutanen da suka san inda ya sauka a kowane lokaci sukan ba shi makwanci, su ciyar da shi, kuma su taimaka masa wajen ci gaba da tafiyarsa, in ji rahoton TRT Word.

Adamu ya yi kokari sosai

Ya samu shiga ta kasashen Netherlands, Jamus, Czech, kuma a halin yanzu yana birnin Istanbul a kasar Turkiyya.

Adam ya kuduri burinsa na zuwa Makka da kafa ne a watan Yuli. Yana shirin bi ta Syria da Jordan.

Hotunansa da aka yada a Instagram sun nuna shi yana daga hannu a kyamara yayin da yake sakin murmushi. Mutane da dama sun mayar da martani kan wannan kyakkyawan niyya.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin abin da mabiyansa ke cewa kamar haka:

noenam ya ce:

"Ta yaya ya iya bin duk wadannan kasashen a hanyar Makka? Bisa a duk isowa? Ina son sani."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

othmanyahyadmg ya ce:

"Ina son irin wannan shawagin."

kutupyildiziiiii ya ce:

"Maşallah dan uwa na Allah'u Teala yayi maka albarka."

france.mosques ya ce:

"Mashallah! Allah ya ida nufi."

deyn_shawket_aqcora_official ya ce:

"Fatan nasara dan uwana, Allah yayi maka jagora."

A wani labarin, kamar yadda duniya ke gani, limaman masallacin Harami a kasar Saudiyya na yin rayuwarsu ta jin dadi ta hanyar samun gata daga masarautar Saudiyya.

Kafar sadarwa ta Al-Haramain Sharifain takan nuna takaitattun bidiyo da kuma yada hotunan abubuwan da ke faruwa a masallatan Harami guda biyu, wanda anan ake yawan ganin malamai cikin sutura ta kawa da rayuwa mai kyau.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta yi duba zuwa ga takaitaccen tarihin daya daga cikin manyan malamai kuma limami a Harami; Sheikh Abdulrahman As-Sudais.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.