Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a

Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a

  • Mutane sun yi gudun tsira da rayuwarsu yayin da rufin ginin wata kotu ya fara rushewa ana tsaka da zaman shari'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa lauyoyi, ma'aikatan kotu da waɗan da ake tuhuma sun yi kokarin fita domin tsira
  • Wata majiya daga ma'aikatar shari'a ta jihar Abia, tace an sanar da gwamnatin jiha domin ɗaukar matakin da ya kamata

Aba, Abia - Mutane sun shiga tashin hankali a Aba, babban birnin kasuwanci na jihar Abia, yayin da ginin wata kotu ya rushe ba zato ba tsammani kusan minti 20 da fara zama.

Vangaurd ta rahoto cewa lamarin ya faru ne ranar Talata da yamma a babar kotun Aba karkashin jagorancin mai shari'a Clinton Okoroafor.

A cewar wani shaida da abun ya faru a kan idonsa, rufin kotun ne ya fara ruguzo wa yayin da mutanen dake ciki da suka haɗa da lauyoyi, ma'aikatan kotu da sauran mutane suka fara gudun tsira.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

Kotu a Aba
Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sai dai har yanzun ba'a gano musabbabin rushewar kotun ba, amma wasu mutane sun alaƙanta shi da rashin ingancin tsarin ginin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya kawo rushewar ginin kotun?

Wasu daga cikin lauyoyin da abun ya faru da su, sun bayyana cewa an gudanar da gyaran ginin shekara uku da suka gabata, "Amma ba'a yi gyaran yadda ya dace ba."

A cewarsu, tun bayan wannan gyara ginin yake zuba wanda haka yasan ruwa yake shiga ginin sosai.

Duk wani kokari na jin ta bakin babban alkalin jihar ya ci tura amma wata majiya a ma'aikatar shari'a ta tabbatar da cewa yasan abinda ke faruwa.

Majiyar ta kuma bayyana cewa shugaban alkalan ya nuna godiyarsa ga Allah kasancewar babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

A cewar majiyar, an sanar da gwamnatin jihar Abia abinda ke faruwa domin ta ɗauki matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

A wani labarin kuma Masarautar Saudiyya ta dakatar da Jiragen Najeriya shiga ƙasar saboda sabon nau'in cutar Omicron

Wani jami'in ofishin jakadancin Saudiyya a Kano yace sun samu umarnin hana jirage tashi domin zuwa Saudiyya.

Sai dai wani babban ma'aikacin kamfanin jiragen sama yace ba zai tabbatar ba saboda wasu jirage biyu sun nufi Jidda yau da safe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262