Aure Babbar Sunnah: Wani matashi ya auri yan mata 9 a rana daya domin nuna musu tsantsar soyayya

Aure Babbar Sunnah: Wani matashi ya auri yan mata 9 a rana daya domin nuna musu tsantsar soyayya

  • Wani matashi ya kafa tarihi a kundin auratayya na duniya, inda ya aure mata 9 a lokaci ɗaya saboda soyayya
  • Saurayin mai suna, Arthur O Urso, ya yi wannan auren ne domin nuna adawarsa ga auren mata ɗaya tilo
  • Auren mata tara da ya yi a rana ɗaya, yasa adadin matansa sun cika 10, kasancewar yana da mata ɗaya kafin nan

Brazil - Wani matashi ɗan kasar Brazil, Arthur O Urso, ya shiga kundin tarihi na duniya bisa auren mata 9 a rana ɗaya saboda soyayya.

Rahotanni sun bayyana cewa Angon kyakkyawa ne sosai abin kwatance, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Ango da mata tara
Aure Babbar Sunnah: Wani matashi ya auri yan mata 9 a rana daya domin nuna musu tsantsar soyayya Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Meyasa Angon ya yi haka?

Mista Arthur ya bayyana cewa babban dalilinsa na yin haka shine don nuna tsantsar soyayya da kuma nuna adawa da auren mace ɗaya tilo.

Kara karanta wannan

Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan aure na mata 9 da kuma angonsu kwara ɗaya ya gudana ne a wata cocin Katolika dake garin Sao Paulo na ƙasar Brazil a nahiyar Latin America.

Kafin wannan aure, shin angon yana da mata?

Tun kafin ɗaura wannan aure da ya kafa tarihi, Arthur yana da mata ɗaya mai suna, Luana Kazaki.

Lokacin da suka fita yawon cin amarci tsakanin Arthur da amaryarsa ta farko Luana, suka yanke shawara kan cewa ya kara auren mata 9 su cika goma.

Ma'auratan sun amince da wannan matakin ne domin nuna wa duniya cewa soyayya ba ta mutum ɗaya bace, ta kowa ce.

Rahotannin da aka tattaro a kafafen sada zumunta, sun tabbatar da cewa Arthur da Luana, sanannu ne a ɓangaren kwarewa a soyayya.

Kazalika ma'auratan sun yi ƙaurin suna wajen yaɗa hotunan su na batsa yayin da suke hutun cin amarci a garin Cap D’Agde na ƙasar Faransa.

Kara karanta wannan

Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo

Wannan birni ya shahara

Wannan birni dake ƙasar Faranta a yankin turawa, ya kasance makura a bariki, kuma har yanzun ana ta cece-kuce a kansa.

A garin dai an haramta yawo da kaya, hakan yasa Arthur da Luana suka ci amarcin su a birnin kuma suna yawon buɗe ido babu tufafi a jikinsu.

A wani labarin kuma An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa an tsinci gawar wasu mutum biyu, mace da namiji a cikin mota.

Hukumar yan sanda tace namijin yana da mata har da ƴaƴa, yayin da ita kuma macen za'a ɗaura mata aure a watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262