'Yan dadi Afrika: Yadda mata 3 suka bar kasashensu na turai suka kauro Afrika, Najeriya
Yayin da wasu 'yan Afirka suka rasa dalilin da ya sa za su ci gaba da kasancewa a cikin kasashensu a nahiyar, wasu fararen fata, musamman mata, da alama sun fi sha'awar Afirka.
Wasu daga cikin wadannan matan sun sami kansu a Afirka kwatsam kuma sun kaunaci nahiyar, amma ga wasu, shawara suka yanke su dawo Afrika dindindin.
Legit.ng ta tattaro cewa wasu mata turawa guda 3 da gangan ko kuma kwatsam suka tsinci kansu a kasashen Afirka amma suka so ta suka dauke ta a matsayin gida.
1.Juliana Belova
Juliana Belova na daya daga cikin 'yan matan da suka yanke shawarar da ba kowa ne zai iya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baturiyar ta tattara kayanta ta yanke shawarar zuwa Nigeria bata waiwaya ba tun daga nan.
Baturiyar 'yar kasar Rasha wadda aka fi sani da suna Oyinbo Marlian a Najeriya ta bar kasarta zuwa Najeriya da N41,000 kacal.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta yanke shawarar da ba a saba gani ba, Juliana ta ce ta bar kasar Rasha ne saboda sha'awarta da wasan kwaikwayo na Najeriya.
Tana daya daga cikin masu kirkirar wasannin kwaikwayo na ban dariya a Najeriya a halin yanzu.
2. Thessa Bagu
A daya bangaren kuma Thessa Bagu ta zauna a Najeriya tun shekaru 15 da suka gabata amma ba haka kawai ba.
A cewar matar 'yar kasar Holland, ta zo Najeriya ne a shekarar 2006 domin hutun shekaru 2, amma ta kasance tana son kasar da al’ummarta.
Ta ce kasar ta sauya rayuwarta zuwa ga mai kyau duk da kalubalen da ta ke fuskanta.
3. Stephanie Fuchs
Ga Stephanie Fuchs, soyayya ta fada, amma ba a Najeriya ba - a Tanzaniya.
Matar Bajamushiya wacce ta dira Tanzaniya a shekara ta 2011 a matsayin ma'aikaciyar bincike a wani sansani, amma ta kamu da soyayya da wani mutum dan kasar.
Wani kamfani zai biya makudan kudade ga mai son ya kalli wasu fina-finai 13
A bangare guda, Akan kalli fina-finai domin nishadi da debe kewa, hakazalika da ma bata lokacin zama ba aikin komai, amma kun taba tunanin akwai fim din da zaku kalla kuma a biya ku kudade?
Wani kamfanin hada-hadar kudi zai ba da $1,300 (N534,950.00) ga duk wanda ke son zama ya kalli wasu manyan fina-finai masu ban tsoro da aka taba yi a duniya.
A cewar CNN, kamfanin mai suna FinanceBuzz yana bincike ne don sanin ko girman kasafin kudin fina-finan yana tasiri da yadda tasirinsa yake ga masu kallo.
Asali: Legit.ng