Latest
Wata Kotun yanki mai zama a Kubwa ta kawo ƙarshen zaman aure tsakanin Hafsat Abdullahi da Adesegun Rufai bayan shafe shekaru huɗu suna raya sunnah.
Wata mata da ba a kai ga tantance bayananta ba ta rasa rayuwarta yayin da wata Kwantena ta kutto daga kan tirela, ta murkushe ta ba zato ba tsammani a Anambra.
Gwamnan jihar Ƙatsina, Alhaji Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu yana taimakon ƴan bindiga a jihar.
Gwamnatin tarayya ta koka kan yadda abubuwa suka taru suka mata yawa ita kaɗai babu mai kama mata, ta ce abu ya kai inda ya kai domin da ƙyar take biyan albashi.
Gwamnatin jihar Sokoto karƙashin gwamna Ahmed Aliyu ta ɗauki nauyin tura ɗalibai 15 'yan asalin jihar zuwa China su karanto kwasa-kwasan injiniyarin.
Daga karshe dai an yi wa marigayi magajin garin Zazzau gatan da ake wa kowane Musulmi idan kwanansa ya ƙare, an masa Sallah kuma an kai shi makwanci.
Wata budurwa ƴar Najeriya ta bayyana cewa ta auri mijin da take so wanda ya kwanta mata a zuciya, inda ta ƙi yarda da batun masu cewa tsoho ta aura.
Wata surika ta tiƙi rawa tare da surikinta lokacin da ake shagalin bikin aurensa da ɗiyarta. Amma ɗiyarta ba ta ji daɗin hakan ba inda ta kalla cike da baƙin ciki.
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya nada sabbin shugabanni guda biyu da za su ja ragamar ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya.
Masu zafi
Samu kari