
Latest







Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, wanda shugaban ƙasa ya dakatar, ya buƙaci babbar kotun tarayya mai zama a Legas ta bada belinsa bisa dalilai guda tara.

Majalisar wakilai ta amince da ƙarin farashin kuɗin man fetur zuwa N617 kan kowace lita duk da kiraye-kirayen da ƴan Najeriya ke yi na a dakatar da ƙarin kuɗin.

Rundunar sojoji a jihar Plateau ta ce ta kama shanu da awaki fiye da dubu daya da ke gararanba a gonakin mutane tare da yi musu barna a karamar hukumar Mangu.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ganin ta kara albashin ma'aikatan Najeriya.

JIhohi biyar ne hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana cewa sun fi kowace jiha a Najeriya sayen kayayyakin abinci da tsada. Cikin jihon akwai jihar Kwara.

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta dauki mummunan mataki a kan kungiyoyin 'yan kasuwa dake kara farashin kayayyaki da na masarufi babu gaira babu dalili a Najeriya.

Wani batun ƙarya na yawo a soshiyal midiya cewa Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon soja Manjo Dr. Hamza Al-Mustapha a matsayin shugaban hukumar tsaro ta DSS.

Hukumar zabe INEC ta gaza kare nasarar da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya samu a babban zaben gwamna ranar 18 ga watan Maris, a gaban kotun ƙarar zabe.

Wani matashi da ya arce da wata mota ta naira miliyan 55 a kwanakin baya a Abuja, ya bayyana cewa ba da nufin sata ya dauki motar ba. Ya ce kawai dai ya tafi.
Masu zafi
Samu kari