Latest
Ana da labari Jam’iyyar PDP ta bukaci INEC ta sake wani zabe tun da ‘yan majalisan Ribas sun dawo APC, ta ce ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas sun rasa kujerunsu.
Shirin tsige Gwamnan Ribas ya yi sanadiyyar da ‘yan majalisar dokoki suka sauya sheka zuwa APC. Kuma an ji matsayar Nyesom Wike a PDP a gwamnatin APC.
Takarar Atiku Abubakar a zabe mai zuwa ta na cikin hadari. Bode George ya ce a zaben 2027, babu wanda zai nemi tikitin jam’iyyar PDP sai mutanen yankin kudu.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa wadanda su ka mutu a harin bam a Kaduna sun mutu su na masu karanta kalmar shahada inda ya ce zai tallafa musu.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya shiga ganawar gaggawa da majalisar zartarwa a jihar bayan sauya sheka na 'yan majalisu 27 zuwa APC daga PDP.
Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu ma'aurata, Aisha Malkohi da mijinta, Abubakar Mahmoud kan zargin badakalar makudan kudade har miliyan 410 a Kano.
Bayan ziyarar da ya kai zuwa Tudun Biri, Malam Nasir El-Rufai da mutanensa sun je Daura. Watanni da barin mulki, tsohon Gwamna El-Rufai ya hadu da Muhammadu Buhari.
An kai hari a Gidan Shaho washegari aka koma kauyen Nasarawar Zurmi inda aka yi asarar mutane, rayuka, dukiya da abinci. Yanzu Mutane sun tsere da suka koma Zamfara
Wasu miyagun yan bindiga sun kai sabon farmaki a jihar Cross Rivers inda suka yi awon gaba da wani babban basarake. Sun kuma halaka mutum daya a harin.
Masu zafi
Samu kari