Masana'antar Fina Finai Ta Girgiza, Ƴar Wasan Fim Ta Bar Duniya bayan Fama da Jinya
- Fitacciyar jarumar fim a masana'antar Nollywood ta rasu bayan doguwar rashin lafiya da ta yi fama da shi na wani lokaci
- Kafin rasuwarta, ‘yan fim da jama’a sun bayar da gudummawa da addu’o’i domin ceto rayuwarta, amma lamarin ya kara tabarbarewa
- Iyalanta sun bukaci jama’a da su daina tura kudade, tare da godiya ga duk wadanda suka mara mata baya a lokacin jinyarta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos - Fitacciyar jarumar Nollywood, Ajara Lasisi ta rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya mai tsanani.
Jarumar da aka fi sani da wacce aka fi sani da Aunty Ajara ta yi bankwana da duniya bayan fama da jinya.

Source: Instagram
An yi rashin jarumar fim a Najeriya
Darekta a Nollywood, Tobi Oladele Teemony ya sanar da rasuwarta ta hanyar wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
A cewar sanarwar, Aunty Ajara ta rasu da dare bayan ta yi doguwar gwagwarmaya da rashin lafiya cikin jarumta da hakuri.
Teemony ya bayyana cewa marigayiyar ta samu kauna, addu’o’i da kuma tallafin kudi daga mutane masu tausayi a sassa daban-daban na duniya.
Ya ce suna matukar godiya ga dukkan wadanda suka tsaya mata tsayin daka da addu’a, gudummawa, kwarin gwiwa da tausayi a lokacin jinyarta.
Haka kuma, ya bukaci jama’a da su daina tura kudade zuwa asusun da aka rika amfani da shi wajen kula da lafiyarta, yana cewa ba a bukatar karin kudade.
A cewarsa, tunaninsu da addu’o’insu na tare da iyalanta, masoyanta da kuma dukkan wadanda wannan rashi mai radadi ya shafa.
Sanarwar ta zo ne tare da wani bidiyo daga yayanta, Ridwan Lasisi, wanda ya tabbatar da rasuwarta bayan likitoci sun sanar da su.

Source: Instagram
An godewa al'umma kan gudunmawarsu
Ridwan ya gode wa ‘yan uwa, ‘yan fim, da ma shugaba da dukkan yan masana’antar fina-finai bisa goyon bayan da suka bayar.
Ya kuma sake rokon jama’a da su daina tura kudade, yana cewa an rufe asusun gudummawar tunda Ajara ta riga ta rasu.
Rasuwar marigayiyar ta faru ne wata guda bayan ‘yan Nollywood sun yi kira na gaggawa domin neman karin taimako, sakamakon tsananin tabarbarewar lafiyarta.
Rahotanni sun nuna cewa Aunty Ajara na dauke da ciki, tare da fama da cutar hanta, inda aka sanya ta kan na’urar taimaka wa numfashi a asibiti.
Fitattun jarumai kamar Wumi Toriola, Mide Martins, Afeez Owo da Ronke Oshodi Oke sun taka rawa wajen neman taimako domin ceto rayuwarta.
Jarumar Fim na neman taimako
Kun ji cewa jarumar Nollywood Halima Abubakar ta bayyana cewa tana fama da ciwon kwakwalwa tare da fuskantar matsanancin rashin matsuguni.
Ta ce ta kashe dukiyar da ta tara wajen yi wa mahaifiyarta tiyata da ta lakume Naira miliyan 9, lamarin da ya kara tsananta mata rayuwa.
Halima ta yi kira ga fitattun ’yan Najeriya da suka hada da Seyi Tinubu da al’umma baki daya da su taimaka mata da kudin jinya da matsuguni.
Asali: Legit.ng

