Jarumar Fim Ta Fito Karara Tana Neman Miji bayan Shafe Shekara 48 ba Aure
- Fitacciyar mawakiya kuma ’yar wasar kwaikwayo, Tamar Braxton, ta bayyana damuwarta kan kasancewa ba ta da aure duk da kaiwa shekaru 48
- Ta danganta halin da take ciki da rashin samun 'nagartattun maza', tana jaddada cewa burinta shi ne samun namiji nagari da zai dace da matsayin aurenta
- Tamar ta kuma amince cewa halayyarta ta mace mai aji na iya tsoratar da wasu maza, amma ta ce tana kokarin sauya dabi’ar domin ta zama mai sassauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Shahararriyar mawakiya kuma ’yar fim Tamar Braxton ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda har yanzu take rayuwa ba tare da aure ba duk da kaiwa shekaru 48 a duniya.
Jarumar wasan kwaikwayon ta bayyana cewa wannan lamari yana bata rai matuka, ganin cewa a fahimtarta, ta riga ta cika sharudan zama matar kirki tun da dadewa.

Source: Instagram
Vanguard ta wallafa cewa Tamar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi inda ta bude zuciyarta kan rayuwar soyayya da kuma kalubalen da take fuskanta wajen samun abokin zama.
Jarumar fim, Tamar na neman mijin aure
Tamar Braxton ta bayyana cewa babban dalilin da take ganin ya hana ta yin aure shi ne rashin samun irin mazan da take bukata.
Ta ce a fahimtarta, maza masu halaye nagari sun yi karanci, yayin da yawancin wadanda take haduwa da su ba su cika burinta ba.
A kalamanta, ta ce ita mace ce da ta cancanci zama matar aure, ba ta da wasu halaye da za su rage mata kima idan ana neman mata ta gari.
Tamar ta kuma amince cewa halayyarta ta mace mai aji, wadda ke da kwarin gwiwa da iya tsayawa kan ra’ayinta, na iya zama dalilin da ke hana wasu maza neman aurenta.

Source: Instagram
Tribune ta rahoto cewa jarumar ta bayyana cewa wasu mazan na iya jin tsoron neman aurenta ta saboda suna ganin ba za su iya cika sharudan da ta ke bukata ba.
Sai dai ta bayyana cewa a halin yanzu tana kokarin rage wannan dabi’a, tana kokari a kullum don zama mai taushi da sassauci.
Tarihin jaruma Tamar Braxton a takaice
An haifi Tamar Estine Braxton a ranar 17, Maris, 1977, a Severn, Maryland, a kasar Amurka. Ita ce karama a cikin 'ya'yan Braxton, inda ’yar uwarta Toni Braxton ta shahara a fagen wakoki.
Rahotanni sun nuna cewa ta fara harkar waka ne tun farkon shekarun 1990 a matsayin mamba a rukunin wakoki na ’yan’uwa mata.
Daga bisani ta shiga harkar waka kai tsaye da kuma talabijin, inda ta zama sananniya wajen waka, wasan kwaikwayo da shirye-shiryen talabijin.
Duk da nasarorin da ta samu a aikinta, Tamar ta nuna cewa har yanzu tana fatan samun nasara a bangaren rayuwar aure, inda ta ce burinta shi ne ta zama matar aure kamar yadda ta dade tana fata.
Bidiyon tsiraicin jaruma Mayo ya bazu
A wani rahoton, kun ji cewa fitacciyar jarumar fim a Najeriya, Mayo Lawal ta yi bayani bayan fitar bidiyon tsiraicinta a shekarun baya.
Jarumar ta bayyana cewa lamarin ya tayar mata da hankali, inda ta daina shiga kafafen sada zumunta domin nema wa kanta mafita.
Ta ce bayan shafe lokacin mai tsawo, ta samu kwanciyar hankali tare da gano kurakuranta da yadda za ta fuskanci rayuwa a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


