Jarumar Fim da Bidiyon Tsiraicinta Ya Bazu a Intanet Ta Yi Magana
- Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Moyo Lawal, ta bayyana yadda bidiyon tsiraicinta da ya fita ya yi mata mummunan tasiri a rayuwa
- Ta ce ta ɗauki hutu domin samawa kanta sauki, yin nazari a kan rayuwa da kuma fara sabon babi mai cike da natsuwa da sauyin dabi’u
- Jarumar ta kuma jaddada cewa an dauki bidiyon da ya fita ne yardarta a wancan lokacin, amma ba tare da izininta ba aka yada shi a duniya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya, Moyo Lawal, ta sake bayyana yadda fitar bidiyon tsiraicinta a baya ya sauya yanayin rayuwarta gaba ɗaya, musamman a ɓangaren tunani.
Ta ce bidiyon tsiraicinta da ya bazu a kafafen sada zumunta a shekarar 2023 ya jefa ta cikin matsanancin hali da kuncin rayuwa sosai.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Moyo Lawal, wadda aka sani da kwarin gwiwa da fara’a a bainar jama’a, ta bayyana cewa lamarin ya sa ta ji rauni matuƙa, har ta yanke shawarar janyewa daga shiga jama’a da kafafen sada zumunta.
Tasirin bidiyon tsiraicin jarumar fim
A wani rubutu da ta wallafa a bikin zagayowar ranar haihuwarta, 1, Janairu, 2026, jarumar ta ce ta tsinci kanta a wani sabon babi na rayuwa, inda ta fi mai da hankali kan gyaran hali da sake tsara manufar rayuwarta.
A bayanin da ta yi, Moyo Lawal ta bayyana cewa bidiyon da ya fita ya yi mata mummunan tasiri a ɓangaren lafiyar kwakwalwa da zuciya.
Ta ce lokacin ne karo na farko da ta ji rauni da gazawa a rayuwa, abin da ya sa ta fahimci cewa samun mafita na zuwa ta hanyoyi daban-daban.

Source: Instagram
Jarumar ta kara da cewa lokacin da ta shafe tana nesa da jama’a ya kasance mai muhimmanci, domin ya ba ta damar yin nazari a kan rayuwarta, fahimtar kura-kuranta.
Martanin masu sukar Moyo a Intanet
Bayan fitar bidiyon, ra’ayoyin jama’a sun kasu gida-gida. Wasu sun nuna mata goyon baya da tausayi, yayin da wasu kuma suka ɗaura mata alhakin abin da ya faru, suna sukar yadda take yawan bayyana kanta a kafafen sada zumunta.
Sai dai jarumar ta bayyana cewa sukar da aka yi mata ya ƙara mata damuwa a zuciya, amma a ƙarshe ta koyi ware abin da zai taimaka mata daga abin da zai ƙara mata raɗaɗi.
Moyo Lawal ta yi barazana daukar mataki
A wani rahoton da BBC ta wallafa a shekarar 2023, lokacin da bidiyon ya fita, Moyo Lawal ta yi barazanar ɗaukar matakin doka.
Ta jaddada cewa bidiyon na sirri ne, an ɗauke shi ne a cikin alakar soyayya a wancan lokacin, ba don ya shiga idon jama’a ba.
Moyo Lawal ta musanta jita-jitar da ke cewa ita ce ta saki bidiyon da gangan, tana mai cewa watsa bidiyon ba tare da izininta ba babban laifi ne.

Kara karanta wannan
Yunkurin juyin mulki: Yadda sojoji suka kama Shehin malami, Khalifa Zariya a Abuja
Auren jarumar fim a Najeriya ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa fitacciyar jarumar fim, Anita Joseph ta sanar da mutuwar aurenta da MC Fish Michael a wani sako da ta fitar.
A sanarwar da ta fitar, jarumar ta bayyana cewa bata da lokacin amsa wasu tambayoyi game da wadanda za su yi magana a kan lamarin.
Maganar da Anita Joseph ta yi ya kawo karshen rade-radin da aka shafe lokaci ana yi a kafafen sada zumunta game da aurenta.
Asali: Legit.ng

