Jarumar Kannywood Ta Ɓare Sabuwar Mota Ta Kimanin N50m, Mutane Sun Mata Rubdugu

Jarumar Kannywood Ta Ɓare Sabuwar Mota Ta Kimanin N50m, Mutane Sun Mata Rubdugu

  • Jarumar masana'antar Kannywood, Maryam Yahaya ta samu sabuwar motar Marsandi da ake tsammanin ta kai kimanin Naira miliyan 50
  • Sayen mitar fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ya yi wa masoya da masu fatan alheri daɗi bayan labarin ya bazu
  • Jarumar ta wallafa hotunan motar a shafukanta na kafafen sada zumunta, inda mutane suka mata rubdugun sakon taya murna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood, Maryam Yahaya ta sayi sabuwar motar hawa.

Matashiyar jarumar wacce ta yi fice bisa yadda ta iya gudanar da kowane irin aiki da aka ba ta a shirin fim, ta mallaki mota Marsandi.

Jaruma Maryam Yahaya.
Jarumar Kannywood,.Maryam Yahaya ta yi sabuwar mota Hoto: @Maryam_Yahaya
Asali: Twitter

Maryam Yahaya ta wallafa hotunan sabuwar motar a shafukanta na kafafen sada zumunta kamar Tuwita da kuma Instagram.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maryam Yahaya ta godewa Allah SWT

"Godiya ta tabbata ga Allah," in ji jaruma Maryam Yahaya yayin da wallafa hotunan motar a shafinta.

Tuni dai masoya da ƴan uwa suka fara taya ta murnar wannan abin alheri, wasu na ƙara jaddada yadda jarumar ke burge su a shirye-shiryen fina-finan Hausa.

Shafin Kannywood Empire wanda ke yawan kawo labarin abubuwan da suka shafi masana'antar shirya fina-finan Hausa ya wallafa labarin sayen motar Maryam.

A ɗan gajeren sakon da ya fitar a Instagram, ya ce Jaruma Maryam Yahaya ta mallaki danƙarerriyar mota da ake tunanin ta kai kimanin Naira miliyan 50.

Saƙon ya ce:

"Masha Allah, Jaruma Maryam Yahaya ta mallaki dankareriyar Mercedes Benz ta kusan Naira miliyan 50, Allah ya sanya alheri."

Mutane sun yi mata rubdugun sakon murna

Umar Abubakar Nafson Guy ya ce:

"Allah ya sanya alheri ƴa kauda idon maƙiya."

Yahanasu Aliyu ta maida martani da cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

"Ana maganar Safeera ta auri Ahmed XM ina ruwan mu da masu sayen mota, mu kam muna can muna murnar auren masoya."

King Mahdi ya ce:

"Ah ah ah Maryama ina taya ki murna, Allah ya sa albarka ya karo dubunsu."

Umar Usman ya ce:

"Masha Allah muna taya ki murna, Allah ya tsare ya sa a kashe lafiya."

Hadiza Gabon ta ba ƴan mata shawara

A wani rahoton, kun ji cewa jaruma Hadiza Aliyu Gabon ta wallafa wani saƙo a shafinsa wanda ke ba ƴan mata shawarin mazan da za su iya aure.

A sakon da jarumar ta Kannywood ta fitar, ta buƙaci mata su aure ko mazajen aure ne, ba dole sai samarinsu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel