Rahama Sadau Ta Faɗi Sunan Wanda Ya Kama Hannunta, Ya Shigo da Ita Kannywood

Rahama Sadau Ta Faɗi Sunan Wanda Ya Kama Hannunta, Ya Shigo da Ita Kannywood

  • Jaruma Rahama Sadau ta ce Ali Nuhu ne ya kawo ta Kannywood, bayan ya ganta tana rawa a wani gidan rawa a jihar Kaduna
  • Fitacciyar jarumar ta fara koyon rawa a makarantar sakandare, inda ta shiga ƙungiyoyin rawa a Kaduna kafin ta shiga harkar fim
  • A wata hirar da Aminu Sherif Momo, Rahama Sadau ta bayyana cewa baiwar rawa da take da ita ce ta ba ta damar shiga Kannywood

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitacciyar 'yar wasan kwaikwayo, Rahama Sadau ta yi magana kan yadda ta shigo masana'antar Kannywood da abin da take yi kafin nan.

Sabanin yadda wasu jarumai ke kawo kansu masana'antar, ita Rahama Sadau ta ce wani ne ya riko hannunta ya shigo da ita Kannywood.

Rahama Sadau ta yi magana kan yadda Ali Nuhu ya shigo da ita masana'antar Kannywood
Rahama Sadau ta bayyana sunan Ali Nuhu a matsayin wanda ya kawo ta Kannywood. Hoto: realalinuhu, rahamasadau
Asali: Instagram

Ali Nuhu ya kawo Rahama Sadau Kannywood

Kara karanta wannan

'Ku dage da addu'a;" Malamin addini ya hango abin da zai faru da Najeriya a 2025

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar ta da Aminu Sherif Momo a shirin Kundin Kannywood, wanda Arewa_Light ya wallafa bidiyon a shafinsa na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Sherif Momo ya tambayi Rahama Sadau ko ita ma zuwa Kannywood ta yi da kafafunta, inda ta ce masa:

"Dauko ni aka yi aka kawo ni."

Da Momo ya tambaye ta wanda ya kawo ta, sai cewa ta yi:

"Ali Nuhu."

Inda Ali Nuhu ya hadu da Rahama Sadau

Rahama Sadau ta sanar da cewa Ali Nuhu, wanda yanzu shi ne shugaban hukumar finafinai ta Najeriya ya gan ta ne a wani gidan rawa, sai ya dauko ta ya shigar da ita fim.

Jaruma Rahama, wacce a yanzu ta yi kaurin suna a harkar finafinan Hausa da na Kudancin Najeriya ta ce:

"Ban san shi ba. Wata rana ne ya same ni ina rawa, sai ya ce ai wanda zai iya rawa zai iya fim."

Kara karanta wannan

Saurayi ya siyawa wata fitacciyar 'yar TikTok gidan N55m a Kano, ta saki bidiyo

Yadda Rahama Sadau ta fara rawa

Momo ya tambayi Rahama Sadau yadda ta koyi rawa, inda ta shaida masa cewa ta fara koya ne a makarantar sakandare.

"A sakandare na fara koyon rawa, na shiga irin kungiyoyin nan na makaranta. Da na gama sakandare sai na shiga wata kungiyar 'yan rawa a Kaduna.
"Muna yin rawar Indiya da kuma irin rawar gefen titin nan da ake yi."

Rahama Sadau ta ce ba ta taba tunani ko a mafarki za ta hadu da jarumai irinsu Momo ba.

Har yanzu, akwai alaka mai karfi tsakanin Ali Nuhu da Rahama Sadau wanda ake yi masu kallon gwanaye a wasan kwaikwayo.

Rahama Sadau ta yi rawar ban mamaki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rahama Sadau da Umar M Shareef sun ja hankalin 'yan Kaduna a bikin sabuwar shekara da aka gudanar a Murtala Square.

A bidiyon da Umar M Shareef ya wallafa, an ga jaruman biyu suna nishadantar da mahalarta taron ta hanyar rera waka da rawa mai kayatarwa.

Kara karanta wannan

Hotuna: Matar fitaccen mawakin Kannywood, Ado Gwanja ta haifo santalelen yaro

Jaruma Rahama Sadau ta taka rawa ta ban mamaki tare da bibiyar wakokin Umar M Shareef kamar Rariya da Rayuwa Ta, lamarin da ya faranta ran jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.