Sabuwar Rigima a Kannywood: Adam Zango Ya Zargi Wani Darakta da Cinye Kudin Marayu
- Adam A. Zango ya zargi wani daraktan Kannywood da cin N550,000 na iyalan marigayi El-Muaz Birniwa, ya nemi ya fito da kudin
- Jaruma Zee Zango wadda ta jaddada ikirarin Zango, ta ce an kai wa iyalan El-Muaz wani kaso na kudin amma an cinye sauran
- To sai dai daraktan da ake magana a kai ya fito ya ce ce zai maka Adam A Zango a kotu, a wani yunkuri na kare kansa daga zargi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Sabuwar rigima ta kunno kai a Kannywood, yayin da Adam A Zango ya zargi wani darakta da cin kudin iyalan marigayi El-Muaz Birniwa.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto wani daraktan Kannywood ya yiwa mawakan masa'antar kaca-kaca kan shirya casu 'yan kwanaki da rasuwar El-Muaz.
A wani sako da ya daraktan ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya zargi mawakan da nuna halin ko in kula da mutuwar El-Muaz.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darakta ya yi wa mawakan Kannywood tatas
Daraktan ya yi ikirarin cewa a cikin mawakan da suka shirya casun, akwai wadanda marigayi El-Muaz ya taimaka wa, wadanda ake ganin kamar ma aminansa ne.
A zantawar Legit Hausa da mai ba da umarnin, ya ce:
"A ce mawaki dan uwansu, ya fadi ya rasu, a bikin mawaki dan uwansu, kuma su tafi su ci gaba da hidindimunsu, kamar ba su mutunta waka, mawaki da kuma dan uwansu ba.
"A cikin mutanen nan, kashi 99 sun mori El-Mu'az, kuma su ne suke tsalle suke dira a wajen casun. Akwai wanda ya ce Allah ya jikan El-Muaz Birniwa, a ci gaba da gashi."
Adam Zango ya zargi darakta da cin kudin marayu
To sai dai da alama kalaman wannan darakta ba su yi wa mawaki kuma jarumi Adam A. Zango dadi ba, inda ya yi masa zazzafan martani.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 24 ga Disamba, Adam A Zango ya nuna cewa daraktan ya yi sama da fadi da kusan N550,000 na marayu.
A wasu hotuna masu dauke da rubutu da ya wallafa, an ga hoton rubutun da daraktan ya yi a hannun hagu, sai kuma hoton rubutun martanin da Zango ya yi a dama.
A martanin da Zango ya yi, ya ce:
"Allahu akbar, ashe tawa da sauki. Ni dai ban ci kudin marayu ba. Don Allah ka fito da N550,000, aminin gaskiya."
Darakta zai yi karar Adam A Zango
'Yan awanni da ikirarin Adam A Zango, daraktan da yake magana a kansa, ya fitar da sabuwar sanarwa a shafinsa na Instagram, inda yake nuna cewa za su hadu kotu da Zango.
A yayin da ya wallafa hoton 'shari'a', daraktan ya ce "mu hade a can malam."
To sai dai kuma, jarumar Kannywood, Zainab Salis Muhammed (Zee Zango) ta fito ta jaddada ikirarin Adam A Zango na cewa daraktan ya ci kudin marayun da ake magana a kai.
A shafinta na Instagram, Zee Zango ta ce:
"Ni fa kudin da ake magana na marayu na ga kudin kuma an ce ranar addu'ar bakwai za a kai su, to iyalan mai rasuwa sun ce an kai wasu ba a kai wasu ba."
Da alama dai wannan rigimar za ta dan dauki lokaci ana yinta, amma ana ganin cewa idan manyan masana'antar, irinsu Ali Nuhu suka saka baki, komai zai iya lafawa.
Hadiza Gabon ta saki bidiyonta da El-Muaz
A wani labarin, mun ruwaito cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta sanarwa duniya irin radadin da take ji na mutuwar El-Muaz Birniwa.
A wani bidiyo da ta saki a shafukanta na sada zumunta, an ga Hadiza Gabon da marigayi El-Muaz a wajen wani wajen kallon wasanni suna wasa da dariya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng