Neman Tabarraki: Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Najeriya, Ali Nuhu Ya Ziyarci Sarkin Kano

Neman Tabarraki: Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Najeriya, Ali Nuhu Ya Ziyarci Sarkin Kano

  • Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya ziyarci mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa dake garin Kano
  • Ali Nuhu ya kai wa Sarkin Kanon takardar nada shi mukami da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tare da neman tabarraki
  • Da yake godiya da jinjina ga basaraken mai daraja ta daya, Ali ya roki Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka daura masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya kuma babban jarumi a masana'antun Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu ya kai ziyarar ban girma fadar mai martaba sarkin Kano.

Ali Nuhu ya ziyarci Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero domin neman tabarraki daga wajensa tare da sanar masa da sabon mukamin da ya samu a gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano zai je ya samu Tinubu su yi kus-kus kan wata gagarumar matsala 1 tak

Ali Nuhu ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin Kano
Neman Tabarraki: Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Najeriya, Ali Nuhu Ya Ziyarci Sarkin Kano Hoto: realalinuhu
Asali: Instagram

Fitaccen jarumin dai yana daya daga cikin sabbin daraktoci 11 da gwamnatin Tinubu ta nada a ma'aikatar raya al'adu ta kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Nuhu ya jinjinawa sarkin Kano

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, shugaban hukumar fina-finan ta kasa ya yi godiya da jinjina ga basaraken kan addu'o'i da shawarwarin da ya ba shi a yayin ziyarara.

Ya kuma roki Allah da ya yi masa jagora tare da sanya wannan mukami da aka ba shi ya zamo masa alkhairi.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Godiya da jinjina ga Mai Martaba Sarkin Kano @hrh_aminu_ado_bayero CRR CNOL JP da irin adduo'i da shawarwari da aka bamu.
"Allah ya bamu ikon yin biyayya a matsayin mu na ya' ya', Ya kuma ja da ran sarki, Allah ya rika da hannayenka bijahi rasulillah sallalahu alaihi wa sallam.

Kara karanta wannan

"Ba ku tsira ba": Fitaccen malamin addini ya aika muhimmin sako ga Tinubu, ya gargadi 'yan siyasa

"Allah ya sa wannan mukami ya zama alheri, ya kuma kare mu daga duk wani sharri da ke tare da shi."

Jama'a sun yi martani

realummy_ ta yi martani:

"Sarki agaban sarki "

mrs_hajia_jml ta ce:

"Amin Amin Allah sa a gama lafiya Yallabai Sir @realalinuhu."

nuracostume ya yi martani:

"Allah ya kara nasara mai girma MD."

saeefjibreel ya ce:

"Ameen. Ya Allah, Muna Maka fatan alheri da nasarori."

amuscap ya ce:

"Sarki da sarki"

real_abdul_mohd_fkd:

"Sai da Kai Shugaba Allah yakara Lafiya."

real_amir_jibrin:

"Allah ya raya riko amin summa amin "

algoniarab:

"Allah ya qara dafa maka Yallabue MD."

Ali Nuhu ya gana da Hannatu Musawa

A gefe guda, Legit Hausa ta kawo a baya cewa ministar Raya Al'adu ta kasa, Hannatu Musawa ya nada a masana'antarta.

Musawa ta karbi bakuncin fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu, Aisha Augie, Otunba Biodun Ajiboye da sauransu a ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng