Kyawawan hotunan barka da sallah daga gidan ango Lilin Baba da amaryarsa Ummi Rahab

Kyawawan hotunan barka da sallah daga gidan ango Lilin Baba da amaryarsa Ummi Rahab

  • Hotunan wankan sallah na amarya Ummi Rahab da angonta mawaki kuma jarumi Lilin Baba sun kayatar da masoyansu
  • A sabuwar wallafar da angon yayi, ya saka hotunansu wurin guda 10 cike da nishadi da farinciki shi da amaryarsa
  • An dai daura auren masoyan ne a tsakiyar watan Yuni da ya gabata a wani matsakaicin biki da aka yi a jihar Kano

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kyawawan hotunan wankan sallah na amarya Ummi Rahab tare da angonta Shuaibu Lilin Baba sun bayyana.

A wata wallafa da mawakin ango Lilin Baba yayi a shafinsa na Instagram, ya zuba zankada-zankada hotunan shi tare da kyakyawar amaryarsa jaruma Ummi Rahab.

Ummi Rahab da Lilin Baba
Kyawawan hotunan barka da sallah daga gidan ango Lilin Baba da amaryarsa Ummi Rahab
Asali: Instagram

Cike da farin ciki tare da kyalli irin na amare zukekiyar jarumar ta bayyana a hotunan.

Tana sanye da atamfa mai launin bula yayin da angonata ya ke sanye da farar shadda mai dinkin babbar riga.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An dai daura auen masoyan ne a tsakiyar watan Yunin 2022 ba tare da an yi wasu jerin bidi'o'i duk kuwa da cewa angonata yana da kumbar susa.

Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

A wani labari na daban, alkawarin Allah ya cika a tsakanin jarumi kuma fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu'aibu Ahmed Idris, wanda aka fi sani da Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa, jaruma Ummi Rahab.

A yau Asabar 18 ga watan Yuni, ne dubban jama’a suka shaida daurin auren manyan jaruman guda biyu.

An yi shagulgula da dama domin raya wannan rana inda amarya Ummi ta fito shar da ita saboda tsabar kyawu da haduwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng