Wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi

Wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi

  • Wani ma'aikaci ya kai karar jaruma Hadiza Gabon gaban Kotun Shari'ar Musulunci kan ta karya masa alƙawarin aure
  • Bala Musa ya shaida wa Kotun sun jima suna soyayya da Gabon kuma ta masa alƙawarin aure, shiyasa da ta nemi Kuɗi yake tura mata
  • Lauyan da ke kare Gabon ya roki Kotu ta bashi isasshen lokaci domin ya zo da wacce yake karewa

Kaduna - Wani mutumi ɗan shekara 48 ma'aikacin gwamnati, Bala Musa, ya maka Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon a gaban Kotun Shari'ar Musulunci da ke Kaduna ranar Litinin.

Daily Trust ta rahoto cewa Mutumin ya kai ƙarar jarumar ne saboda ta ƙi aurensa duk da kuɗaɗen da ya kashe a kanta.

Bala Musa ya shaida wa Kotun cewa sun jima suna murza soyayya da Jarumar kuma ta masa alƙawarin zata aure shi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta karyata zaban Lawan a matsayin ɗan takarar Maslaha

Jaruma Hadiza Gabon.
Wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi Hoto: @adizatou
Asali: Instagram

Ya faɗa wa Kotun cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daga lokacin da muka fara soyayya zuwa yanzun na kashe mata kuɗi N396,000. Duk lokacin da ta nemi kuɗi ina bata ba tare da damuwa ba ina fatan wataran zamu yi aure."
"Ta gaza zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara inda nake zaune bayan na kammala duk wasu shirye-shiryen tarbarta."

Hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa a ranar 23 ga watan Mayu aka fara sauraron ƙarar, amma Hadiza Gabon ba ta samu halarta ba.

Shin Jarumar ta amsa laifinta?

Lauyan Hadiza, Mubarak Kabir, ya shaida wa Kotun cewa wacce yake kare wa ta gaza tabbatar da gaskiyar sammacin Kotu da aka kai mata.

Lauyan ya faɗa wa Kotu cewa:

"Wacce nake karewa ba fitacciyar mace ce da ke mu'amala da mutane daban-daban da niyya daban-daban. Ta na matuƙar kula da lafiyarta da tsaron kanta."

Kara karanta wannan

Abin da 'yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023, Yahaya Bello

Bayan haka Ƙabir ya roki Kotun ta ba shi lokaci isasshe domin ya gabatar da wacce yake karewa a gaban Kotu.

Alƙalin Kotun mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2022.

A wani labarin na daban kuma Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Wasu daga cikin Jaruman Kannywood da tauraruwarsu ke haskawa sun bayyana tsayawa takarar siyasa a zaɓen 2023.

Mun tattaro muku waɗan nan jaruman da suka nuna sha'awar ba da gudummuwarsu a ɓangaren shugabancin al'umma a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262