Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai

Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai

  • Wasu sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya sun bayyana yayin da ta warke sumul kamar bata kwanta jinya ba
  • Jarumar ta koma bakin harkokinta inda a yanzu haka ta tafi shakatawa a kasar Dubai
  • A bidiyon, an gano Maryam tare da kawarta cikin shiga ta riga da wando da kuma kallabi a kanta a wani wajen shakatawa

Shahararriyar jarumar Kannywood wacce ta yi fama da matsananciyar rashin lafiya, Maryam Yahaya ta samu sauki sosai, inda ta koma bakin harkokinta na yau da kullun.

A yanzu haka jarumar ta lula kasar Dubai inda take shakatawa tare da kawayenta.

A cikin wasu bidiyo da hotuna da ta wallafa a shafinta na Instagram, an gano jarumar sanye da riga da wando yayin da take shanawa a wani wajen shakatawa a kasar Larabawan.

Kara karanta wannan

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai
Jikin Maryam Yahaya ya yi kyau Hoto: real_maryamyahaya
Asali: Instagram

Kuma jikinta ya murmure sosai a yanzu sabanin ramar da ta yi a wasu hotunanta da suka dunga yawo a soshiyal midiya a kwanakin baya.

Jarumar dai ta sha fama da rashin lafiya wanda ya janyo aka dunga cece-kuce, yayin da wasu suka ce ta samu shafar aljanu ne, wasu kuma suka ce jifa aka yi mata.

Sai dai a hira da aka yi da ita a lokacin, Maryam ta bayyana cewa cutar Typoid da Malaria ne ke damunta.

Kalli bidiyon nata a kasar Dubai kamar yadda ta wallafa a shafinta:

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

A wani labarin, mun ji cewa mawakin Kannywood, Naziru Sarkin waka ya tare da yayyensa da ke masana'antar shirya fina-finan sun yi wa dattijuwar jaruma, Ladin Cima kyautar kudi naira miliyan biyu.

Kara karanta wannan

TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba

Naziru a cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce sun yi mata kyautar wannan kudi ne domin ta ja jari ta yadda za ta dunga samun na cin abinci. Ya kuma ce idan Allah ya barsu da rai za su dunga tallafa mata lokaci zuwa lokaci.

Hazalika ya ce an tura masa bidiyon abokiyar sana'arsa Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow inda take ta raddi kan furucin da yayi a baya game da yadda ake lalata da mata a masana'antar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng