Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar

Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar

  • Jaruman fina-finai na masana’antar Kannywood sun gabatar da taro na musamman don yin addu’o’i ga abokan ayyukan su da suka rasu
  • An yi taron ne a anguwar Gyadi-gyadi da ke cikin birnin Kano kamar yadda Gidauniyar Kannywood wacce ake kira da Kannywood Foundation ta shirya
  • Manyan mutane masu mukamai daban-daban a gwamnati, masu fada a ji a masana’antar, sababbi da tsofaffin jarumai sun halarci taron

Kano - Jaruman masana’antar fina-finai ta Kannywood sun gabatar da wani taro na musamman don yin addu’o’i ga abokan aikinsu da suka riga mu gidan gaskiya.

Kamar yadda fina-finan Hausa ya wallafa a Facebook, Gidauniyar Kannywood wacce aka sani da Kannywood Foundation ce ta shirya taron a cibiyar matasa da ke anguwar Gyadi-gyadi a cikin Kano.

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Shekaru 6 da kawo TSA domin hana sata, har gobe ana tafka barna

Mutane da dama masu mukamai a gwamnati, masu ruwa da tsaki a masana’antar, manyan mutane, tsofaffi da sababbin jaruman masana’antar duk sun samu halartar taron tare da kuma jama’ar gari.

Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar
Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar. Hoto daga Fina-finan Hausa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar
Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar. Hoto daga Fina-finan Hausa
Asali: Facebook

Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar
Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar. Hoto daga Fina-finan Hausa
Asali: Facebook

Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar
Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar. Hoto daga Fina-finan Hausa
Asali: Facebook

Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar
Hotunan jaruman Kannywood da suka shirya taron addu’a ga mamatan masana'antar. Hoto daga Fina-finan Hausa
Asali: UGC

Fitattun Jaruman Kannywood 4 da suka rigamu gidan gaskiya a 2021

A wani labari na daban, yayin da muke bankwana da 2021, mun tattaro muku jerin wadannan jarumai da suka rigamu gidan gaskiya da kuma fatan Allah ya jikansu da rahama.

1. Sani Garba SK

A ranar Laraba, 15 ga Disamba, 2021, Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood Sani Garba wanda aka fi sani da Sani SK rasuwa.

BBC Hausa ta ruwaito cewa jarumin ya rasu ne a birnin Kano, bayan doguwar jinyar da yayi.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: EFCC ta gurfanar da ‘babban yaro’ Mompha, ana zargin ya saci Naira Biliyan 6

Rahoton yace fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar da rasuwar ɗan wasan.

2. Ahmad Tage

Allah Ya yi wa fitaccen jarumi kuma mai daukar hoto a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Alhaji Aliyu Ahmad Tage rasuwa.

Ahmad Tage ya rasu ne a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba a jihar Kano bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

3. Zainab Booth

Tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Zainab Musa Booth ta rasu ne a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli a jihar Kano.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shahararrun ’yan wasan Hausa uku wato Maryam Booth, Ramadan Booth da kuma Amude Booth.

An yi jana’izarta a safiyar Juma’a, 2 ga watan Yuli, da misalin karfe 8:00 a gidanta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng