Kannywood: Tauhidi muka koya wa mutane a wakar dawo-dawo ta Labarina Series, Naziru Sarkin Waka ya magantu

Kannywood: Tauhidi muka koya wa mutane a wakar dawo-dawo ta Labarina Series, Naziru Sarkin Waka ya magantu

  • Sarkin Waka ya bayyana cewa wakar da ya yi a shiri mai dogon Zango 'Labarina Series' tana ɗauke da Tauhidi ne tsantsa
  • Naziru M Ahmad, wanda yana ɗaya daga cikin jaruman da ke taka rawa a shirin, yace yana matukar son wakar ta dawo-dawo
  • Yace ya sha wahala sosai kafin ya samu nasarar kammala wakan, kuma ba wani shiri ya yi ba sanda ya yi wakan

Kano - Ɗaya daga cikin jaruman dake taka rawa a shirin 'Labarina Series' kuma fitaccen mawaki, Nazir M Ahmad, yace Tauhidi ne tsantsa a wakarsa ta dawo-dawo.

Yayin wata fira da BBC Hausa, Naziru wanda aka fi sani da sarkin waka, yace saboda tauhidin wakar ne ma yake matukar son ta.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan wani matashi da ya ci F9 a darussan NECO, Ya kammala digiri da daraja ta farko

Sumayya da Sarkin Waka
Kannywood: Tauhidi muka koya wa mutane a wakar dawo-dawo ta Labarina Series, Naziru Sarkin Waka ya magantu Hoto: @aminusaira
Asali: Instagram

Sarkin waka yace:

"Bani da wata waka da nake alfahari da ita kuma nake ji da ita saboda nasarar da na samu na saka Tauhidi a cikin ta irin wannan wakar ta Dawo-Dawo gaskiya."

Wace waka ce ta dawo-dawo?

Sarkin waka ya rera wakar ne a shirin fim mai dogon zango na masana'antar Kannywood, mai suna 'Labarina Series' wanda ɗan uwansa, Malam Aminu Saira, ya bada umarni.

A cikin shirin Labarina, an saka wakar dawo-dawo ne a lokacin da mawakiya Sumayya (Nafisa Abdullahi) ke kokarin ganin masoyinta ya dawo gida.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzun tun bayan sakin wakar, aƙalla mutum miliyan 1.7m ne suka kalle ta.

Ko ya haɗu da kalubale wajen wakar?

Shahararren mawakin ya bayyana cewa tabbas ya fuskanci kalubale da ya caza masa kai bayan ya kammala wakar.

Kara karanta wannan

Matashi ya samu kyautar N41k yayin da ya mayar da N4m da ya tsinta a lalita a kan hanya

A cewarsa masu ɗan hannu ne suka fara jefa shi cikin matsala, yayin da suka sace na'urar da ya aje wakar bayan kammala ta.

Bugu da kari yace ya sha matsin lamba daga yayansa, Aminu Saira, kan nemo wakar, sai da kyar ya samu ya haɗa komai.

Naziru yace:

"Ba wani shiri wakar dawo-dawo take da shi ba, kawai dai waka ce ta shirin Labarina mai dogon zango."

A wani labarin kuma Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.

Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262