Labaran duniya
Ibraheem El-Zakzaky ya bayyana cewa kusan jirgi daya ya dauko mutanen Nijar da na Najeriya, ya ja-kunne a kan shirin aukawa makwabta da yaki da sunan ECOWAS.
Shugabannin ƙungiyar ECOWAS sun gana bayan cikar wa'adin da suka ba Janar Abdourahamane Tchiani ya tattara kayansa ya sauka daga kan madafun ikon ƙasar Nijar.
Gwamnatin sojoji da Janar Abdourahamane yake jagoranta a Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin kulle sararin samaniyar kasar bisa tsoron mamayar da za a kawo.
Hedikwatar hukumar tsaron ta ƙasa ta fito ta yi magana kan batun cewa Shugaba Bola Tinubu, ya shirya amfani da ƙarfin soja kan sojojin juyin mulki na Nijar.
Justin Trudeau, Farai Ministan Canada ya rabu da matarsa, Sophie, bayan sun shafe shekaru 18 suna zaman aure. Trudeau ya sanar da hakan a shafinsa na Instagram.
A wani mataki na ƙoƙarin dawo da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar, Najeriya ta katse wutar lantarkin da take ba ƙasar. Hakan ya jefa birane da dama a duhu.
An nunawa Bola Tinubu amfani da ƙarfin soja wajen dawo da farar hula a Nijar zai jawo masifa. Idan tarzoma ta tashi a Jamhuriyyar, ‘yan gudun hijira za su shigo
Duk da zuwan mulkin dimokuraɗiyya, kasashen Afrika da dama na ci gaba da fuskantar ƙalubale na mulkin soja. Ana yawaitar samun juyin mulki a cikin kasashen.
Faransa ta sanar da cewa za ta tura jiragen sama su kwashe yan kasarta da sauran kasashen Turai daga Nijar. Hakan na zuwa ne bayan juyin mulki da soji suka yi.
Labaran duniya
Samu kari