Labaran duniya
Tawagar da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS), ta sake tura wa zuwa Nijar ba ta haɗu da shugaban gwamnatin sojojin ƙasar ba.
Kasashen Burkina Faso da Mali masu ƙawance da Jamhuriyar Nijar sun aike da jiragen yaƙinsu zuwa Nijar domin taimaka wa ƙasar kan barazanar yaƙi da ECOWAS ke yi.
Fasinjojin jirgin sama 271 da suka taso daga birnin Miami zuwa Chile sun gamu da tashin hankali, matuƙin jirgin saman da suke ciki ne ya rasu ana tsaka da gudu.
Shugabannin rundunonin tsaron ƙasashen ƙungiyar ECOWAS, sun bayyana cewa a shirye suke su kutsa kai jamhuriyar Nijar domin dawo da mulkin dimokuradiyya a ƙasar.
Wani babban kuskure a ɓangaren IT a bankin Ireland ya sanya mutanen da ba su da kuɗi a asusun su za su iya cirar kuɗi masu yawa har N833k idan suka je ATM.
Shugabannin rundunonin tsaro na ƙungiyar ECOWAS, za su gudanar da taro a makon nan da muke ci a birnin Accra na Ghana domin duba yiwuwar amfani da ƙarfin soji.
Shugaba Tinubu na Najeriya kuma shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, ECOWAS, na duba yiwuwar tura sojoji zuwa Jamhuriyar Nijar.
Sabon Firaministan jamhuriyar Nijar da sojojin juyin mulkin ƙasar suka naɗa, Ali Mahaman Lamine Zeine, ya bayyana cewa ƙasar za ta tsallake duk wasu takunkumai.
Sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum za su tuhumi tsohon shugaban ƙasar a gaban kotu bisa zargin cin amanar ƙasa da ake yi a kansa.
Labaran duniya
Samu kari