Abubuwa Sun Sukurkucewa Trump, Ya Sake Yin Rashin Nasara a Amurka

Abubuwa Sun Sukurkucewa Trump, Ya Sake Yin Rashin Nasara a Amurka

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya san matsayarsa kan wata karar da ya shigar a gaban kotun tarayya da ke Florida
  • Alkalin kotun ya yanke hukunci kan karar wadda Trump ya shigar da wata jarida yana neman a biya shi $10bn
  • Mai shari'a Darrin P. Gayles ya ki amincewa da bukatar da Trump ya gabatar amma ya ba shi zabi kan abin da zai yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Wani alƙali ya yi watsi da ƙarar ɓata suna ta dala biliyan 10 da Shugaba Donald Trump ya shigar.

Donald Trump ya shigar da karar ne kan jaridar Wall Street Journal da Rupert Murdoch, game da wani labari da aka wallafa kan alaƙarsa da Jeffrey Epstein.

Trump ya yi rashin nasara a kotu
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Jaridar Associated Press ta kawo rahoton hukuncin kotun ne a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

An barke da murna a Amurka bayan kayar da abokin Trump a zaben kasar Hungary

Wane hukunci aka yanke a karar Trump

Alƙalin kotun, Darrin P. Gayles da ke Florida, ya rubuta a cikin takardar hukuncin cewa Trump ya gaza gabatar da hujjojin da ke nuna cewa an wallafa labarin ne da nufin yin ƙeta.

Sai dai, alƙalin ya ba shugaban ƙasar na Amurka damar sake gyara ƙarar tasa don sake shigar da ita, tashar Sky News ta kawo rahoton.

Meyasa Trump ya shigar da kara?

Trump ya shigar da ƙarar ne a watan Yulin 2025, biyo bayan alƙawarin da ya yi na kai jaridar kotu jim kaɗan bayan ta sake yin labari kan tsohuwar alaƙarsa da Epstein.

Jaridar ta wallafa wani labari da ke bayyana wata wasiƙa mai nuna batsa, wadda ta ce tana ɗauke da sa hannun Trump, kuma tana cikin wani kundin hoto da aka haɗa wa Epstein a bikin cikarsa shekaru 50 a duniya a 2023.

Daga baya majalisar dokokin Amurka ta fitar da wasiƙar ga jama'a, bayan ta dauko takardun daga gidan Epstein.

Kara karanta wannan

Trump ya yi wa Fafaroma Leo wankin babban bargo bayan masa nasiha kan Iran

Trump ya musanta rubuta wasiƙar, inda ya kira labarin da "ƙarya, ƙeta, da kuma ɓata suna."

Lauyoyin jaridar da na Murdoch sun buƙaci mai shari'a Gayles da ya yanke hukuncin cewa bayanan da ke cikin labarin gaskiya ne, don haka ba za a kira su ɓata suna ba.

Trump ya yi rashin nasara a kotu
Shugaba Donald Trump a wajen yakin neman zabe Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Amma alƙalin ya rubuta cewa:

"Ko Shugaba Trump ne marubucin wasiƙar ko kuma shi abokin Epstein ne, waɗannan tambayoyi ne na zahiri waɗanda ba za a iya tantance su ba a wannan mataki na shari'ar."

Trump ya gamu da cikas

Wannan hukunci ya zama wani babban cikas ga ƙoƙarin gwamnatin Trump na shawo kan kurar da ta tashi bayan fitar da bayanan sirri na Epstein, da kuma yunƙurin shugaban na yin amfani da tsarin shari'a don tsoratar da kafafen yaƙa labarai da ke sukar sa.

Har zuwa yanzu, Fadar White House da kuma kakakin Dow Jones ba su bayar da wani martani kan wannan hukunci ba.

Gwamnatin Trump ta yaba wa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Shugaba Donald Trump kan harkokin kasashen Larabawa da Afirka, Massad Boulos ya yabawa gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Putin ya kira takwaransa na Iran a waya, an ji abin da suka tattauna tsakaninsu

Amurka ta yaba wa gwamnatin Najeriya bisa jajircewarta wajen gaggauta shari’o’in da suka shafi ta’addanci da sauran laifuffuka masu alaƙa da shi.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta samu nasarar yanke hukunci ga mutane 386 da ake zargi da ta’addanci bayan gudanar shari’a a kotun taayya da ke Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng