Kasar Afrika Ta Gargadi Iran, za Ta Tura Sojoji 500,000 Su Kwace Tehran
- Hafsun sojan kasar Uganda, Muhoozi Kainerugaba ya sake cika baki game da yakin da Amurka ta hada baki da Isra'ila ta kaddamar a Iran
- Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa zai tura dakarun sojoji 500,000 domin su kwace Tehran, babban birnin kasar Iran, su mika ga Isra'ila
- Sojan ya yi magana ne a daidai lokacin da aka sanar da tsagaita wuta domin samun damar tattaunawa tsakanin kasashen Amurka da Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Uganda - Kasar Uganda da ke nahiyar Amurka ta kara tsoma baki a yakin Isra'ila/Amurka da Iran da ake a yankin Gabas ta Tsakiya.
Bayan maganar da babban sojan Uganda, Muhoozi Kainerugaba ya yi a kwanakin baya, ya sake cewa a shirye suke su tura dakaru kasar Iran.

Kara karanta wannan
Shugaba Putin ya kira takwaransa na Iran a waya, an ji abin da suka tattauna tsakaninsu

Source: Twitter
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Muhoozi Kainerugaba ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yayin da aka fara tattaunawa domin kawo karshen yakin.
Isra'ila: Uganda za ta tura sojoji Iran
Babban hafsan rundunar sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, ya sake jawo hankalin duniya bayan wasu sakonni guda biyu da ya wallafa cikin ‘yan sa’o’i.
A bayanin da ya yi, ya bayyana shirinsa na tura dubban sojojin Uganda domin kare Isra’ila tare da iƙirarin cewa yana da gagarumin rundunar matasa da suka shirya shiga yaƙi da za su iya mamaye Tehran.
Roya News ta rahoto cewa a sakonsa na farko, Janar Kainerugaba ya rubuta cewa:
“A shirye nake in tura sojojin Uganda 100,000 zuwa Isra’ila, ƙarƙashin jagoranci na, domin kare ƙasa mai tsarki, ƙasar Yesu Almasihu!”
Daga bisani, ya ƙara da wani sako mai ƙarfi inda ya ce:
“Ina da kusan matasa 500,000 masu son yaƙi. Abin da suke so kawai shi ne kuɗi. Za su iya kwace Tehran kyauta ga Isra'ila.”
Maganar Uganda kan Iran a baya
Tun da farko a watan Maris na shekarar 2026, Janar Kainerugaba ya nuna goyon baya ga Isra’ila a yaki da Iran, inda ya ce:
“Duk wani kokari na cin galaba kan Isra’ila zai jawo mu cikin yaƙi, muna tare da Isra’ila!”
Janar Kainerugaba mai shekaru 51, ɗa ne ga shugaban Uganda, Yoweri Museveni, kuma ana kallonsa a matsayin mai yiwuwa ya gaji kujerar shugabancin kasar a gaba.

Source: Getty Images
A matsayinsa na Shugaban rundunar UPDF, ya shahara wajen fitar da ra’ayoyi kai tsaye da kuma jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan harkokin duniya.
Amurka ta zargi China game da Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Amurka ta zargi kasar China da shirin tallafawa Iran da makamai ta bayan fage.
Hakan na zuwa ne yayin da kasashen Iran da Amurka suka zauna a teburin sulhu a kasar Pakistan amma ba a cimma wata matsaya ba.
Amurka ta ce China za ta iya ba Iran makamai ta hanyar amfani da wasu kananan kasashe ta tura su Tehran, amma ba za ta zuba ido ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
