Yakin Iran: Fafaroma Leo Ya Yi wa Trump Zazzafan Martani kan Sukar Shi

Yakin Iran: Fafaroma Leo Ya Yi wa Trump Zazzafan Martani kan Sukar Shi

  • Fafaroma Leo ya yi wa shugaban Amurka martani kan sukar shi da ya yi bayan wata nasiha da ya masa game da yake-yake
  • A hira da aka yi da shi, Fafaroman ya sanar da cewa shi ba dan siyasa ba ne kuma ba zai ji tsoron fadawa wani shugaba gaskiya ba
  • A ranar Lahadi da dare ne shugaba Donald Trump ya caccaki Fafaroma Leo, yana cewa bai fahimci yanayin siyasar duniya ba a yau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Vatican - An fara musayar yawu tsakanin shugaban Amurka da Fafaroma Leo XIV kan yake-yaken da Donald Trump ke yi a duniya.

Fafaroma Leo ya yi wa Donald Trump martani bayan sukar da shugaban Amurka ya masa a daren Lahadi, inda ya zarge shi da goyon bayan Iran.

Kara karanta wannan

Trump ya ba duniya mamaki, ya fito kamar Yesu Almasihu a hoto

Fafaroma Leo da shugaba Donald Trump
Donald Trump a hagu, Fafaroma Leo a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Fafaroma ya yi wa Trump raddi

Rahoton da Vatican News ta wallafa ya nuna cewa Fafaroma Leo ya yi wa Donald Trump raddi ne a daidai lokacin da zai shiga jirgi zuwa nahiyar Afrika.

Fafaroma Leo XIV ya amsa tambayoyi dangane da kalaman Donald Trump, yana mai cewa:

“Ni ba ɗan siyasa ba ne kuma zan gaba da magana ina adawa da yaƙi da neman zaman lafiya ta hanyar tattaunawa.”

Ya ƙara da cewa:

“Ba na ganin ya dace a yi amfani da saƙon littafi mai tsarki ta hanyar da wasu ke yi. Zan ci gaba da yin magana kan yaƙi, da ƙoƙarin ƙarfafa zaman lafiya, tattaunawa da haɗin kai tsakanin ƙasashe domin nemo mafita ga matsaloli."
"A yau mutane da yawa na shan wahala, rayukan marasa laifi da dama sun salwanta, kuma ina ganin dole ne wani ya tsaya ya ce akwai hanya mafi kyau maimakon yaki.”

Kara karanta wannan

Trump ya yi wa Fafaroma Leo wankin babban bargo bayan masa nasiha kan Iran

Fafaroma Leo yana shirin tafiya Afrika
Fafaroma Leo yana shirin tafiya Afrika daga Vatican. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kiran Fafaroma kan zaman lafiya

Rahoto ya nuna cewa daga nan ya sake maimaita kira kan zaman lafiya da ya fara da shi tun daga farkon shugabancinsa, yana cewa:

“Ina faɗa wa dukkan shugabannin duniya, ba shi [Trump] kaɗai ba: mu kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, mu ƙarfafa zaman lafiya da sulhu.”

A martaninsa ga wata tambaya daga wani ɗan jarida daga Amurka, Fafaroman ya bayyana cewa ba ya jin tsoron gwamnatin Trump ko yin magana da littafi mai tsarki.

NBC ta rahoto ya ce:

“Mu ba ‘yan siyasa ba ne,”
“Ba mu kallon manufofin ƙasashen waje kamar yadda shi zai iya fahimta, amma ina da cikakken imani da saƙon littafi mai tsarkki a matsayin mai kawo zaman lafiya.”

Trump ya fito a Yesu Almasihu

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya wallafa hoton da ke nuna shi a matsayin Yesu Almasihu.

Kara karanta wannan

Trump Ya Fadi abin da Zai Faru da China idan Ta Kuskura Ta Tura wa Iran Makamai

A hoton da ya wallafa, Trump ya nuna kan shi tare da wani haske, wasu kamar mala'iku a saman shi da wasu sojoji tare da tutar Amurka.

Baya ga haka, ya nuna ya tunkari wani maras lafiya yana kwance zai kai masa dauki, lamarin da ke nuna zai warkar da mutumin ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng