'Sai dai a Mutu,' Kasar Cuba Ta Daina Jin Tsoron Trump, Ta Shirya Yaki da Amurka
- Shugaban Cuba, Miguel Díaz-Canel, ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin kare ƙasarsa daga barazanar harin sojin Amurka
- Cuba na fuskantar matsanancin ƙarancin wutar lantarki da abinci bayan Amurka ta toshe hanyoyin samar da man fetur ta hanyar shirin OSS
- Donald Trump ya gindaya sharuɗɗan saukar Díaz-Canel daga mulki tare da yin zaɓe, yayin da Cuba ta ce ba za ta taba amince wa da Amurka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Cuba – Shugaban ƙasar Cuba, Miguel Díaz-Canel, ya bayyana cewa ƙasarsa tana shirin ko-ta-kwana domin tunkarar harin soji daga ƙasar Amurka.
Miguel Díaz-Canel ya jaddada cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin kare Cuba daga duk wata barazanar Amurka da Trump.

Source: Getty Images
Cuba ta shirya yin yaki da Amurka
Yayin wata hira da gidan talabijin na NBC a ranar Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026, Díaz-Canel ya ce babu wani dalili da zai sa Amurka ta ƙaddamar da hari ko ƙoƙarin sace shugaban ƙasa.
"Idan hakan ta faru, za a fafata, za mu kare kanmu, kuma idan ya zama dole mu mutu, za mu mutu," in ji shi, yana mai nakalto kalmomi daga taken ƙasar Cuba.
Tun a watan Disamban da ya gabata, Amurka ta ƙarfafa matakan killace ruwan ƙasar Venezuela a ƙarƙashin shirin 'Operation Southern Spear', wanda hakan ya yanke hanyoyin samar da man fetur ga Cuba.
Wannan matakin ya jefa Cuba cikin mummunan rashi na wutar lantarki da fargabar ƙarancin abinci.
Hakazalika, Gwamnatin Trump ta huro wuta a kan cewa lallai sai Shugaba Díaz-Canel ya sauka daga muƙaminsa, a cewar rahoton New York Times.
Rashin amanar Amurka ga Cuba
Sai dai Díaz-Canel, wanda shi ne shugaba na farko da ba ɗan gidan Castro ba tun bayan juyin juya halin Cuba, ya ƙi amincewa da wannan buƙatar, yana mai cewa "ba shi da tsoro" kuma zai ci gaba da gwagwarmaya.
Shugaban na Cuba ya bayyana cewa kulla yarjejeniya da Amurka a halin yanzu "abu ne mai matuƙar wahala."
Ya kafa hujja da hare-haren da Amurka ta kai wa Iran a lokacin da ake tsaka da tattaunawa kan batun nukiliya a matsayin shaida cewa ba za a iya amincewa da ƙasar Amurka ba.

Source: Getty Images
Cuba ta zargi Amurka kan halin da take ciki
A ɓangare guda, Amurka ta gindaya sharuɗɗan da suka haɗa da sakin fursunonin siyasa, barin jam'iyyu da dama su fafata a zaɓe, da kuma ba wa kafafen yaɗa labarai ƴancin kai kafin ta janye takunkuman da ta sanya wa Cuba.
Díaz-Canel ya dora alhakin matsalolin tattalin arzikin ƙasarsa kacokan kan abin da ya kira "killace makamashi" da Amurka ta yi musu, yana mai cewa gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa domin inganta rayuwar jama'a.
Trump zai afka wa Cuba da yaki
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump na cigaba da yi wa kasashen duniya barazana inda ya nuna cewa zai dauki matakin soja kan kasar Cuba.
Shugaban Amurka ya bayyana cewa “Cuba kasa ce ta gaba” da zai faramaka bayan ya yi alfahari da nasarorin da sojojin Amurka suka samu a Venezuela da kuma Iran.
Trump bai bayyana takamaiman abin da yake shirin yi game da Cuba ba, amma ya sha cewa gwamnatin Havana, wadda ke fuskantar matsalar tattalin arziki, na dab da rushewa.
Asali: Legit.ng

