Trump Ya Gamu da Matsala, Birtaniya Ta Juya wa Amurka baya a Shirin Killace Iran
- Firayim Minista Keir Starmer ya sanar da cewa Birtaniya ba za ta sa hannu wajen toshe tashoshin jiragen ruwan Iran tare da dakarun Amurka ba
- Donald Trump ya ba da umarnin killace dukkan jiragen da ke shiga ko fita daga Iran bayan rugujewar tattaunawar zaman lafiya a Pakistan
- Farashin ɗanyen mai ya haura dala 100 sakamakon fargabar katsewar hanyoyin samar da makamashi ta mashigar ruwa ta Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Birtaniya – Firayim Minista Sir Keir Starmer ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga cikin shirin Amurka na killace tashoshin jiragen ruwan Iran ta hanyar amfani da dakarun soji ba.
Ko da yake Birtaniya za ta ci gaba da amfani da na'urorin kwashe nakiyoyi da na daƙile jirage marasa matuƙi a yankin, Starmer ya jaddada cewa ba za a yi amfani da jiragen yaƙi ko sojojin Birtaniya wajen toshe hanyoyin ruwan Iran ba.

Kara karanta wannan
Shugaba Putin ya kira takwaransa na Iran a waya, an ji abin da suka tattauna tsakaninsu

Source: Getty Images
Birtaniya ta sake juya wa Trump baya
Da yake magana da kafar yaɗa labarai ta BBC 5 Live, Firayim Ministan ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin an buɗe mashigar ruwa ta Hormuz baki ɗaya domin rage farashin makamashi "cikin gaggawa."
Ya bayyana cewa diflomasiyyar Birtaniya ta mayar da hankali ne wajen ganin mashigar ta kasance a buɗe ga kowa, maimakon a kulle ta.
Wannan takun-saƙa ya biyo bayan sanarwar da Shugaba Donald Trump ya yi, inda ya bayyana cewa Amurka za ta fara toshe dukkan jiragen ruwan da ke ƙoƙarin shiga ko fita daga tashoshin Iran.
Barazanar Amurka na killace Iran
Wannan mataki ya zo ne bayan gazawar tattaunawar zaman lafiya da aka yi a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan.
Rundunar sojin Amurka ta Centcom ta tabbatar da cewa za ta aiwatar da wannan takunkumi kan dukkan jiragen da ke da alaƙa da Iran, kodayake ba za ta takura wa jiragen da ke zuwa wasu ƙashen daban ba.
Trump ya yi iƙirarin cewa ƙasashen ƙungiyar NATO, ciki har da Birtaniya, za su taimaka wajen "gyara" mashigar ta hanyar tura jiragen kwashe nakiyoyi.
Sai dai Sir Keir Starmer ya kauce wa yin sharhi kan ayyukan soji na musamman, yana mai nanata cewa Birtaniya ba ta goyon bayan matakin killace ƙasar Iran.

Source: Getty Images
Tasirin rufe mashigar Hormuz
Mashigar ruwa ta Hormuz ita ce hanya mafi muhimmanci a duniya, inda kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas (LNG) na duniya ke ratsawa ta cikinta, in ji rahoton The Telegraph.
Tun bayan fara hare-haren Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta dakatar da zirga-zirgar jiragen dakon mai ta mashigar, lamarin da ya jefa kasuwannin duniya cikin rudani.
Sakamakon sanarwar killace Iran da Amurka ta yi, farashin ɗanyen mai na Brent ya haura dala 100 a karon farko tun bayan da aka sanar da tsagaita wuta.
Wannan hauhawa na barazana ga tattalin arzikin ƙasashe da dama, ciki har da Birtaniya kanta, inda ake fuskantar matsin lamba kan ƙarin harajin man fetur da gwamnati ke shirin yi a watan Satumba.
Larabawa sun kauce wa taimakon Trump
A wani labari, mun ruwaito cewa, kasashen Larabawa sun fara kauce wa Amurka wajen neman sababbin makamai, bayan hare-haren Iran sun rage musu kayan kariya.
Kasashen sun fara koma wa kasashe kamar Koriya ta Kudu, Ukraine da Birtaniya domin samun sabbin tsarin kariya, ciki har da makamai masu arha da jirage marasa matuka.
Karancin samar da makamai a duniya, musamman a Amurka, ya sa wadannan kasashe ke neman hanyoyi daban, yayin da bukatar makamai ke karuwa sosai.
Asali: Legit.ng

