Muhimman Abubuwan da Suka Faru bayan Tsagaita Wutar Iran, Amurka da Isra'ila

Muhimman Abubuwan da Suka Faru bayan Tsagaita Wutar Iran, Amurka da Isra'ila

Birnin Tehran, Iran - An tsagaita wuta a yakin da ake yi tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasashen sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ne a yakin da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya.g

Amurka da Iran sun kasa cimma yarjejeniya
Shugaba Donald Trump na Amurka da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf Hoto: Nurphoto
Source: Getty Images

Amurka, Isra'ila da Iran sun tsagaita wuta

A daren ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2026, Donald Trump ya bayyana a shafinsa na Truth Social cewa za a tsagaita wuta na tsawon makonni biyu.

Trump ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan buƙatar da Firaminista Shehbaz Sharif da Field Marshal Asim Munir na ƙasar Pakistan suka gabatar masa.

"Na amince zan dakatar da dukan hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu domin ba da sararin kammala yarjejeniyar zaman lafiya."

Kara karanta wannan

"Dole a cika su"; Iran ta gindaya sharudda 2 kafin fara tattaunawa da Amurka

- Donald Trump

Abubuwan da suka faru bayan tsagaita wuta

Legit Hausa ta zakulo wasu abubuwan da suka faru tun bayan tsagaita wutar da kasashen suka yi a yakin da ake yi.

Ga jerinsu nan kasa:

1. Saukar farashin danyen fetur

Farashin danyen mai ya fadi matuka bayan Amurka da Iran sun cimma yarjejeniya ta tsagaita wuta a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Rahoton tashar BBC ya nuna cewa farashin Brent crude ya sauka da kusan kashi 13 zuwa $94.80 a kowace ganga.

2. Kiran a tsige Donald Trump

'Yar majalisar dokokin Amurka, Ilhan Omar ta yi kira a tsige shugaba Donald Trump a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ilhan Omar, ta bayyana cewa akwai bukatar tsige shugaba Donald Trump daga shugabancin da ya ke yi a kasar Amurka.

"Dole ne a tsige Donald Trump daga kan mulki saboda barazanar aikata laifuffukan yaki da kisan kare dangi."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Firaministan Isra'ila ya sake dauko rigima bayan dakatar da yakin Iran

- Ilhan Omar

3. Isra'ila ta ci gaba da kai hari a Lebanon

Dakarun rundunar sojojin Isra'ila sun amince da dakatar da kai hare-hare a Iran amma ban da Lebanon.

A cewar jaridar The Guardian, rundunar ta ce dakarunta za su ci gaba da kai hare-hare da kuma gudanar da ayyukan kasa kan kungiyar Hezbollah a Lebanon.

Gwamnatin Isra’ila ta ce ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, amma ta jaddada cewa yarjejeniyar ba ta shafi Lebanon ba.

4. Rasuwar tsohon Ministan Iran

​Tsohon Ministan harkokin wajen Iran, Dr Kamal Kharrazi, wanda ya samu raunuka a wani hari da aka kai kan gidansa da ke Tehran ya riga mu gidan gaskiya.

Dr Khamal Kharrazi ya rasu
Tsohon Ministan harkokin wajen Iran, Dr Khamal Kharrazi Hoto: @IraninSA
Source: Twitter

Ofishin Jakadancin Iran a kasar Afrika ta Kudu ya wallafa a shafin X cewa Dr Kamal Kharrazi, ya rasu ne a daren ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilun 2026.

Dr Kamal Kharrazi ya yi aiki a matsayin ministan harkokin wajen Iran daga watan Agusta 1997 zuwa Agusta 2005, sannan kuma ya kasance mamba a majalisar tantance muhimman abubuwa na kasar.

Kara karanta wannan

Putin ya sanar da dakatar da yakin da Rasha ke gwabzawa da Ukraine

5. Iran ta gindaya sharuddan tattaunawa

Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohmmad Bagher Ghalibaf, ya gindaya sharuddan tattaunawa da Amurka.

​Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana a shafinsa na X cewa ba za a fara tattaunawa ba har sai an tsagaita wuta a Lebanon.

Hakazalika, Ya bayyana cewa dole ne a tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon da kuma sakin kuɗaɗen Iran da aka rike kafin a fara tattaunawa.

6. Trump ya yi barazanar ci gaba da yakar Iran

​A lokacin da ake shirin tattaunawa a Pakistan, Donald Trump ya yi barazanar ci gaba da yakar Iran idan ba a cimma matsaya ba.

Donald Trump yayin hira da jaridar New York Post, ya bayyana cewa Amurka na sake loda sababbin makamai a jiragen ruwanta na yaki domin kai hari kan Iran idan tattaunawar zaman lafiya ta gaza cimma da mai ido.

7. Tattaunawar Amurka da Iran

A ranar Asabar, 11 ga watan Afrilun 2026, tawagar Amurka da Iran sun tattauna a birnin Islamabad na kasar Pakistan.

Kara karanta wannan

A karon farko, Saudiyya ta yi magana mai muhimmanci da kasar Iran bayan tsagaita wuta

Tashar BBC Hausa ta kawo rahoton tattaunawar da aka fara a tsakanin bangarorin biyu domin neman cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin da ake yi.

Tawagar Amurka ta kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa JD vance, yayin da ta Iran ke karkashin shugaban majalisar dokoki, Mohammad Bagher Ghalibaf.

8. Iran da Amurka sun kasa cimma yarjejeniya

Iran ta Amurka sun kammala tattaunawa ta tsawon sa'o'i 21 a birnin Islamabad ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa tawagar Iran da ta Amurka sun kasa cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Vance ya ce akwai gibi mai girma tsakanin bangarorin biyu duk da tsawon lokacin da aka kwashe ana tattaunawa.

9. Kulle mashigar Hormuz

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa rundunar ruwan kasar za ta fara kulle mashigar Hormuz tare da hana zirga-zirgar jiragen ruwa bayan kasa cimma matsaya tsakanin kasarsa da Iran yayin tattaunawa.

Trump ya bayyyana a shafinsa na Truth Social cewa rundunar ruwan Amurka za ta fara dakile duk wani jirgi da ke kokarin shiga ko fita daga mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Ba boye boye, an ji abin da Saudiyya da wasu kasashe suka yi yayin sulhunta Amurka da Iran

Trump ya gargadi China kan taimakon Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya gargadi China kan taimakon Iran.

Donald Trump ya bayyana cewa China za ta fuskanci manyan matsaloli idan ta aika makamai zuwa Iran.

Gargadin Trump na zuwa ne yayin da aka yi zama domin sulhu kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng