Trump Ya Fadi abin da Zai Faru da China idan Ta Kuskura Ta Tura wa Iran Makamai

Trump Ya Fadi abin da Zai Faru da China idan Ta Kuskura Ta Tura wa Iran Makamai

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi China cewa za ta fuskanci manyan matsaloli idan ta aika makamai zuwa Iran a yayin rikicin yankin
  • Trump ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa mai zurfi da Iran duk da cewa ya ce ba damuwa ko za a cimma yarjejeniya ko a’a
  • Ana gudanar da tattaunawar kasashe uku tsakanin Amurka da Iran da Pakistan bayan tsagaita wuta mai rauni, yayin da rikicin ya girgiza kasuwannin duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin gargadi ga kasar China game da yakin da ake yi.

Trump ya ce China za ta fuskanci manyan matsaloli idan ta aika makamai zuwa Iran, yana mai gargadi kan yiwuwar rikicin ya kara tsananta.

Trump ya yi wa China gargadi kan yakin Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Da yake magana da manema labarai a wajen Fadar White House, Trump ya nuna yanayi mai rikitarwa kan batun Iran, yana cewa ana ci gaba da tattaunawa mai zurfi, cewar CBS News.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi fatali da zaman sulhu da ake yi, ya sake shan alwashi kan Iran

Yadda aka yi zaman sulhu a Pakistan

Wannan na zuwa ne yayin da aka yi zama domin sulhu kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.

Sai dai an tashi baram-baram saboda ba a cimma matsaya ba bayan wakilan kasashen sun hadu a Pakistan.

Trump ya magantu kan yarjejeniya

Trump ya kara da cewa ba shi da damuwa ko za a cimma yarjejeniya da Tehran, yana mai cewa “ko da me ya faru, mu ne masu nasara”.

Trump ya kuma yi ishara da karuwar ayyukan soji a tekun yankin Gulf, yana cewa ana gudanar da aikin share nakiyoyi a mashigar ruwa.

Ya gargadi cewa akwai yiwuwar akwai wasu nakiyoyi a cikin ruwa, lamarin da ke kara nuna hadarin tsaro a yankin.

Trump ya ja kunnen China kan yaki da Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump tare da takwaransa na China, Xi Jinping Hoto: Andrew Caballero Raynolds.
Source: Getty Images

Yadda ake tattaunawa tsakanin Iran da Isra'ila

A halin yanzu, an fara tattaunawar kasashe uku tsakanin Amurka da Iran da Pakistan a ranar Asabar bayan sanar da tsagaita wuta na makonni biyu.

Kara karanta wannan

Sabon shirin yaki: Amurka ta fadi manyan makaman da ta zargi China za ta ba Iran

Wannan rikici ya dauki tsawon makonni bakwai, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da girgiza kasuwannin duniya baki daya.

Tattaunawar ta biyo bayan ganawa daban-daban tsakanin jami’an Amurka da Iran da kuma Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif.

A gefe guda kuma, ana shirye-shiryen wata sabuwar hanya ta diflomasiyya inda ake sa ran tattaunawa tsakanin Isra’ila da Lebanon a mako mai zuwa.

Ana sa ran wannan tattaunawa za ta gudana a birnin Washington, D.C., a matsayin wani bangare na kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

Mashigar Hormuz: Iran ta ƙaryata Amurka

Mun ba ku labarin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi karin haske kan ikirarin Amurka cewa jiragen ruwanta sun ratsa mashigar Hormuz.

Kasar ta bayyana cewa babu wani jirgin Amurka da ya bi ta yankin yayin da ake ci gaba da yarjejeniya tsakanin kasashen biyu.

Tashin hankalin ya ƙaru kan mashigar Hormuz yayin da Iran da Amurka ke musayar zarge-zarge masu karo da juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com