Bayan Tattaunawar Iran da Amurka Ta Rushe, An Harba Wasu Makamai kan Isra'ila

Bayan Tattaunawar Iran da Amurka Ta Rushe, An Harba Wasu Makamai kan Isra'ila

  • An harba makaman rokoki daga kudancin Lebanon zuwa yankin Metula da ke Arewacin Isra'ila, lamarin da ya tashi hankulan Yahudawa
  • Kungiyar Hezbollah ta kuma yi amfani da jirage marasa matuƙi wajen kai hari kan sojojin Isra'ila da aka jibge a yankin Yir’on
  • Wannan sabon tashin hankali ya biyo bayan rugujewar tattaunawar zaman lafiya da aka yi a Pakistan tsakanin Amurka da Iran

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila – Rahotanni sun tabbatar da cewa an harba wasu makaman roka guda biyu daga kudancin ƙasar Lebanon zuwa yankin Upper Galilee da ke arewacin Isra'ila yau Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026.

Hukumar tsaron cikin gida ta Isra'ila (IHFC) ta tabbatar da cewa an kunna ƙararrawar gargaɗi a yankin Metula da ke kusa da iyaka domin ankarar da mazauna yankin su nemi mafaka.

Kara karanta wannan

'Za mu ci gaba da kai hari,' Isra'ila ta sake tsokano Iran da ta kashe mutane a Lebanon

Hezbollah ta harba rokoki da jirage marasa matuƙi kan Isra'ila yau Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026, bayan gazawar tattaunawar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka.

Hezbollah ta harba makaman roka kan Isra'ila
Iran ta yi gwajin makami mai linzami kirar Fateh 110. Hoto: Mohsen Shandiz/Corbis via Getty Images
Source: Getty Images

An harba makamai zuwa Isra'ila

Wannan harin na yau na nuni da ci gaba da takun-saƙa tsakanin dakarun Hezbollah da ke Lebanon da kuma dakarun Isra'ila, wanda ya ƙara tsananta tun bayan fara yaƙin Iran da Amurka da ya shafi yankin gabas ta tsakiya baki ɗaya, in ji rahoton Aljazeera.

Ko da yake ba a bayyana asarar rayuka ko dukiya ba kawo yanzu, wannan mataki ya ƙara rura wutar fargaba ga mazauna arewacin Isra'ila waɗanda suka daɗe suna fuskantar barazanar makamai daga Lebanon.

Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa suna sa ido sosai kan dukkan wani motsi daga kudancin Lebanon kuma a shirye suke su mayar da martani kan dukkan wani hari da aka kai wa yankunansu.

Wannan lamari na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da aka sanar da gazawar tattaunawar zaman lafiya a Pakistan tsakanin Amurka da Iran, wanda hakan ke nuna cewa yakin gabas ta tsakiya zai iya ci gaba da gudana.

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila: Yawan asarar da Amurka ta yi yayin yaki a Gabas ta Tsakiya

Hezbollah ta kai hari kan sojojin Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da Hezbolla ta sanar da cewa ta ƙaddamar da wani hari ta amfani da jirage marasa matuƙi kan dakarun sojin Isra'ila.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya afka wa sojojin ne da ke jibge a yankin Yir’on, wani wuri da ke Arewacin Isra'ila.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram, ta bayyana cewa wannan harin martani ne ga abin da ta kira "zaluncin Amurka da Isra'ila" a kan al'ummar yankin da kuma ƙasar Lebanon.

Hezbollah ta ce za ta ci gaba da kai hare hare Isra'ila don daukar fansa.
Hayaki na tashi daga wani wuri da makamin Isra'ila ya sauka a Kudancin Beirut a ranar 8 ga Afrilu, 2026. Hoto: anwar amro / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Alƙawarin ci gaba da kai hare-hare

Ƙungiyar ta Hezbollah ta bayyana ƙara zafafa hare-haren nata a daidai lokacin da tattaunawar zaman lafiya a Pakistan tsakanin Amurka da Iran ta ruguje ba tare da an cimma matsaya ba.

"Wannan martani zai ci gaba har sai an dakatar da hare-haren Amurka da Isra'ila a kan ƙasarmu da al'ummarmu," in ji sanarwar ƙungiyar.

Yadda aka tashi tattaunawar Iran, Amurka

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, JD Vance, ya sanar da cewa an tashi baram-baram a tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Iran ba tare da cimma matsaya ba.

Amurka ta bayyana cewa ba za ta amince da kowace irin yarjejeniya ba muddin Iran ba ta ba da tabbacin daina kera makamin nukiliya na dindindin ba.

A ɓangare guda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa dama ba su yi tsammanin samun yarjejeniya a zama ɗaya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com