Iran Ta Fadi Babban Abin da Ya Hana Samun Daidaito Tsakanin Kasar da Amurka
- Shugaban Majalisar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi magana game da rashin samun daidaito da aka yi a sulhu a Pakistan
- Ghalibaf ya ce duk da niyyar sulhu, ƙasarsa ba ta da cikakken amincewa da ɓangaren da suke tattaunawa da shi
- Ya kuma yaba wa Pakistan bisa rawar da ta taka wajen sauƙaƙa tattaunawar, yana tura saƙon godiya ga al’ummar ƙasar kan goyon bayan da suka bayar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Shugaban Majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana matsalar da ta jawo aka gaza samun daidaito a sulhu da Amurka.
Ghalibaf ya fitar da sanarwarsa ta farko bayan kammala tattaunawar da aka yi a Islamabad da ke kasar Pakistan.

Source: Getty Images
A cikin jerin saƙonni da ya wallafa a shafin X, Ghalibaf ya ce tun kafin fara tattaunawar ya jaddada cewa Iran na da niyya mai kyau da kuma aniyar cimma matsaya.
Abin da aka tattauna yayin sulhu
Wannan na zuwa ne yayin aka fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya a halin yanzu.
Kasar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa buƙatun Amurka ne suka hana samun maslaha kan batutuwan mashigar Hormuz da fasahar nukiliya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce ba su yi tsammanin cimma matsaya da Amurka a zama ɗaya ba saboda yanayin rashin amana.
An rahoto cewa mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya bar Pakistan bayan sa'o'i 21 na tattaunawa ba tare da sanya hannu kan takarda ba.

Source: Getty Images
Iran ta nuna shakku kan gaskiyar Amurka
Sai dai ya bayyana cewa sakamakon abubuwan da suka faru a yaƙe-yaƙe biyu da suka gabata, ƙasarsa ba ta da cikakken amincewa da ɓangaren da suke tattaunawa da shi.
Ya ƙara da cewa a wannan zagayen tattaunawar, ɓangaren da suke adawa da shi bai samu damar gina amincewa a zukatan tawagar Iran ba.
A cewarsa, wannan rashin amincewa shi ne babban ƙalubalen da ya hana samun cikakken ci gaba a tattaunawar.
Godiya ta musamman da Iran ta yiwa Pakistan
Ghalibaf ya kuma bayyana godiyarsa ga Pakistan, wadda ya kira ƙasa abokiya kuma ‘yar’uwa, bisa taimakon da ta bayar wajen sauƙaƙa gudanar da tattaunawar.
Ya ce yana aika saƙon gaisuwa da godiya ga al’ummar Pakistan, yana mai yaba wa irin rawar da suka taka wajen tallafa wa wannan muhimmin yunkuri na diflomasiyya.
Iran ta karyata Amurka kan mashigar Hormuz
A baya, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi karin haske kan ikirarin Amurka cewa jiragen ruwanta sun ratsa mashigar Hormuz.
Kasar ta bayyana cewa babu wani jirgin Amurka da ya bi ta yankin yayin da ake ci gaba da yarjejeniya tsakanin kasashen biyu.
Tashin hankalin ya ƙaru kan mashigar Hormuz yayin da Iran da Amurka ke musayar zarge-zarge masu karo da juna wanda ke kara rikici a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng

