Ana Batun Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, Netanyahu Ya Daujo Rigima da Wata Ƙasa

Ana Batun Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, Netanyahu Ya Daujo Rigima da Wata Ƙasa

  • Kasar Turkiya ta ɗauki zafi game da kalaman Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan Shugaba Recep Tayyib Erdogan
  • Turkiyya ta soki Netanyahu kan kalaman da ya yi wa Erdogan, tana mai cewa ba shi da halacci ko darajar koyar da kowa dabi'a mai kyau
  • Jami’an Ankara sun zargi Netanyahu da haddasa rikici da tada tashin hankali domin ci gaba da mulki, suna mai cewa dole ne ya fuskanci hukunci kan laifukan da ya aikata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ankara, Turkey - Sabuwar rigima na neman barkewa tsakanin Isra'ila da Turkiyya ana tsakanin da tattaunawa a Pakistan.

Turkiyya ta soki Benjamin Netanyahu kan kalaman da ya yi wa shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan, tana mai cewa kowa ya san ba shi da ɗabi’a ko halaccin yi wa kowa wa’azi.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi fatali da zaman sulhu da ake yi, ya sake shan alwashi kan Iran

Kalaman Netanyahu sun fusata kasar Turkiyya
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan yayin taro a Ankara. Hoto: Anadolu.
Source: Getty Images

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shugaban sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran wanda ya wallafa a shafinsa na X.

Turkiyya ta zargi Netanyahu da kisan gilla

Ya ce Netanyahu, wanda ya shirya kisan kiyashi a Gaza tare da kai hare-hare a ƙasashe da dama, yana kai hari ga Recep Erdogan ne saboda tsananin matsin lamba.

Ya ƙara da cewa Netanyahu mutum ne da ake nema ruwa a jallo bisa takardun kama shi, wanda kuma ba shi da abokai, yayin da manufofinsa ke jefa yankin cikin rikici.

Duran ya jaddada cewa dole ne Netanyahu ya fuskanci hukunci kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa kan bil’adama, yana mai cewa Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan adalci.

Netanyahu ya caccaki shugaban Turkiyya
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Turkiyya ta soki kalaman Netanyahu

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ita ma ta soki Netanyahu, tana cewa kai hari ga Erdogan na nuna rashin jin daɗin gaskiyar da Turkiyya ke faɗa a kowane dandali.

Kara karanta wannan

Trump ya gargadi Netanyahu kan kai hari Lebanon bayan tsagaita wuta

Ta bayyana Netanyahu a matsayin “Hitler na wannan zamani” saboda laifukan da ake danganta masa, tare da nuna tarihin hare-haren da ya yi a yankin.

Sanarwar ta kuma yi nuni da takardar kama da kotun manyan laifuffuka, ICC ta fitar, tana gargadin kokarin Netanyahu na dakile tattaunawar zaman lafiya da kuma manufofin faɗaɗa ikonsa.

Haka kuma ta jaddada kudirin Turkiyya na ganin an hukunta Netanyahu, tare da ci gaba da kare fararen hula marasa laifi da rikice-rikice suka shafa.

Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza tun Oktoba 2023, inda aka kashe dubban Falasdinawa, aka raunata da dama, tare da lalata yawancin gine-ginen rayuwar fararen hula a yankin.

Trump ya gargadi Netanyahu ana maganar sulhu

Mun ba ku labarin cewa Amurka ta yi gaggawar gargadin Benjamin Netanyahu kan hare-haren Isra’ila a Lebanon domin kar ya rusa sharadin tsagaitawa da aka yi da Iran.

Shugaba Donald Trump ya bukaci Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da ya rage yawan hare-haren da ke barazana ga tsagaita wutar.

Hakan na zuwa ne bayan Isra’ila ta ce za ta fara tattaunawa da Lebanon bayan Trump ya aika da saƙo mai ƙarfi ga Netanyahu ta wayar tarho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.