An Tashi Baram Baram: Amurka da Iran Sun Kasa Fahimtar Juna, Ana Iya Komawa Yaki

An Tashi Baram Baram: Amurka da Iran Sun Kasa Fahimtar Juna, Ana Iya Komawa Yaki

  • JD Vance, ya sanar da cewa an tashi baram-baram a tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Iran ba tare da cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi ba
  • Amurka ta bayyana cewa ba za ta amince da kowace irin yarjejeniya ba muddin Iran ba ta ba da tabbacin daina kera makamin nukiliya na dindindin ba
  • A ɓangare guda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa dama ba su yi tsammanin samun yarjejeniya a zama ɗaya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Pakistan – Tattaunawar zaman lafiya da aka kwashe sa’o’i 21 ana gudanarwa a birnin Islamabad tsakanin Amurka da Iran ta ƙare ba tare da cimma wata yarjejeniyar sulhu ba.

Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa tawagar Iran da ta Amurka sun kasa cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ake fafatawa a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi fatali da zaman sulhu da ake yi, ya sake shan alwashi kan Iran

Amurka da Iran sun tashi baram baram a Pakistan
Dakin da aka gudanar da taron tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran a Pakistan. Hoto: Aamir QURESHI / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta zargi Iran a rashin cimma matsaya

Vance ya bayyana cewa duk da sa’o’in da aka shafe ana musayar ra’ayi, har yanzu akwai gibi mai girma tsakanin buƙatun ɓangarorin biyu, in ji rahoton Aljazeera.

Ya jaddada cewa Amurka ta fito da dukkan sharuɗɗan da take da su fili, inda ta nuna wuraren da za ta iya sassautawa da kuma waɗanda ba za ta taɓa canza matsayi a kansu ba.

Babban dalilin da ya janyo aka tashi baram baram shi ne batun shirin nukiliya na ƙasar Iran. Vance ya ce Amurka tana son ƙwaƙƙwaran tabbaci daga Iran cewa ba za ta taɓa kera makamin nukiliya ba, ba wai kawai na ɗan lokaci ba.

"Tambayar a nan ita ce, shin muna ganin jajircewa daga ɓangaren Iraniyawa na kin kera makamin nukiliya, ba yanzu ba, ba nan da shekara biyu ba, amma na dogon lokaci? Har yanzu ba mu ga hakan ba," in ji Vance yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan tashi daga zaman.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Babban abin da Amurka da Iran ke rigima a kai yayin tattaunawa

Kalli bidiyon jawabinsa a kasa:

Martanin Iran: "Rashin amana ya yi tasiri"

A ɓangare guda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa dama ba su yi tsammanin samun yarjejeniya a zaman tattaunawa ɗaya ba, musamman ganin cewa tattaunawar ta zo ne bayan kwanaki 40 na yaƙi da ake yi musu.

Baghaei ya bayyana cewa ko da yake an samu fahimtar juna a wasu fannoni, akwai manyan saɓani a kan muhimman batutuwa guda biyu ko uku, in ji rahoton NBC News.

Ya ƙara da cewa tattaunawar ta haɗa da sababbin batutuwa kamar ikon mallakar mashigar ruwa ta Hormuz da sauran matsalolin yanki. Ya jaddada cewa dole ne diflomasiyyar Iran ta ci gaba da kare haƙƙi da muradin al'ummar ƙasar.

Amurka ta ce Iran ba ta nuna alamar za ta amince da bukatun da aka gabatar mata ba.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance na jawabi ga 'yan jarida jim kadan bayan tattauna wa da wakilan Iran a Pakistan. Hoto: Jacquelyn Martin - Pool/Getty Images
Source: Getty Images

Kiran Pakistan na ci gaba da tsagaita wuta

Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaq Dar, wanda ƙasarsa ce ta karɓi baƙuncin taron, ya buƙaci ɓangarorin biyu da su ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta duk da rashin cimma matsaya.

Kara karanta wannan

Kashe kashe a Najeriya ya damu Atiku sosai, ya yaba wa gwamnatin Amurka

Dar ya yi kira ga Amurka da Iran da su kiyaye "kyakkyawan yanayi" na tattaunawar da kuma yin rantsuwar guje wa kai wa juna hari.

Ya jaddada cewa Pakistan za ta ci gaba da taka rawar gani wajen sauƙaƙe tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu a kwanaki masu zuwa.

Iran ta gano karyar da Amurka ta sharara

A wani labari, mun ruwaito cewa, Iran ta yi karin haske kan ikirarin Amurka cewa jiragen ruwanta sun ratsa mashigar Hormuz.

Kasar Musuluncin ta bayyana cewa babu wani jirgin Amurka da ya bi ta yankin yayin da ake ci gaba da yarjejeniya tsakanin kasashen biyu.

Tun da farko, Iran ta bayyana cewa ta gargadi jiragen ruwan yaƙin Amurka da kada su shiga Hormuz, tare da barazanar kai musu hari idan suka yi kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com