Netanyahu Ya Yi Fatali da Zaman Sulhu da Ake Yi, Ya Sake Shan Alwashi kan Iran

Netanyahu Ya Yi Fatali da Zaman Sulhu da Ake Yi, Ya Sake Shan Alwashi kan Iran

  • Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya jaddada ci gaba da yaki da Iran duk da zaman sulhu da ake yi a Pakistan a yanzu
  • Netanyahu ya jaddada cewa Isra'ila za ta ci gaba da yaƙi da Iran da ƙawayenta, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta ja da baya ba
  • Shugaban ya zargi shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da goyon bayan Iran, tare da danganta shi da abin da ya kira kashe-kashen ‘yan Kurdawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake tayar da kura yayin da ake ci gaba da zaman sulhu tsakanin Iran da Amurka.

Netanyahu ya ayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙi da Iran da ƙawayenta, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa na tinkarar abin da ya kira tsarin ta’addanci.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi babbar barazana 1 da har yanzu Iran take da shi ga kasashen duniya

Tsugune ba ta kare ba tsakanin Iran da Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar 11 ga watan Afrilun shekarar 2026 da muke ciki.

An fara zaman sulhu tsakanin Iran da Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da ake tsaka da sulhu a Pakistan tsakanin wakilan Amurka da na Iran domin tsagaita wuta.

Yayin zaman, Amurka ta amince ta saki wasu kadarorin kasar Iran, lamarin da ya kara karfafa gwiwar kasar wajen ci gaba da tattaunawa.

Wata majiya da ke kusa da tawagar Iran a Islamabad ta ce Amurka ta kuma amince za ta umarci Isra'ila ta rage hare-hare a Lebanon.

Majiyoyi sun nuna cewa an kammala zagayen farko na tattaunawa, da aka kira da mafi sirri idan aka kwatanta da na baya.

Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da kai hari a Iran
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Netanyahu ya yi barazana ga kasar Iran

Netanyahu ya ce Isra’ila ƙarƙashin jagorancinsa ba za ta daina yaƙi da Iran da ƙungiyoyin da take mara wa baya ba.

Kara karanta wannan

Trump ya gargadi Netanyahu kan kai hari Lebanon bayan tsagaita wuta

Haka kuma, ya zargi shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da yin sassauci ga Iran, tare da zarginsa da hannu a abin da ya kira kisan gilla ga ‘yan Kurdawa.

Netanyahu ya yi rubutu kamar haka:

"A karkashin mulki na, Isra'ila za ta ci gaba da kai hari kan mulkin ta'addanci na Iran da kawayenta.
" Sannan Erdogan da ke taimaka masu ta hanyoyi daban-daban, yana taimakawa wurin hallaka yan Kurdawa da ke kasarsa."

Hakan ya zo bayan ma’aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce wasu mazauna Isra’ila sun harbe wani Bafalasdine har lahira a yankin West Bank, lamarin da ke ƙara tayar da hankali a yankin.

Iran ta zargi Amurka kan tattaunawa a

An ji cewa mataimakin shugaban ƙasa na farko na Iran, Mohammad Reza Aref ya yi magana kan yiwuwar gudanar da yarjejeniya.

Aref ya ce sakamakon tattaunawar Islamabad zai dogara gaba ɗaya kan fifikon Amurka a tattaunawar zaman lafiya.

Ya bayyana cewa yarjejeniya mai amfani ga ɓangarorin biyu na yiwuwa idan Amurka ta mai da hankali kan muradunta na fifita kanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.