Kasashen Afirka da Suka Yanke Alaka, ba Su Aminta da Isra’ila a Matsayin Kasa ba
- Batun amincewa da ƙasar Israila na ci gaba da jawo cece-kuce, inda wasu ƙasashen Afirka ke ƙin kulla cikakken alaƙar diflomasiyya
- Ƙasashe irin su Algeria, Libya da Somalia sun ƙi amincewa da Isra'ila a matsayin ƙasa, suna bin sahun ƙasashen Larabawa da Musulmi
- Duk da amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1949, har yanzu wasu ƙasashe na duniya ba su amince da Isra'ila ba, saboda rikici da Falasdinu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Batun amincewa da Isra'ila a matsayin ƙasa na ci gaba da zama abin muhawara a duniya, musamman a Afirka.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu ƙasashe suna ƙin kulla cikakkiyar alaƙar diflomasiyya da kasar Isra'ila saboda zarge-zarge mabambanta.

Source: Getty Images
Kasashen da ke da matsala da Isra'ila
Ƙasashe kamar Algeria, Libya da Somalia sun ƙi amincewa da Isra'ila gaba ɗaya, suna nuna adawa mai tushe daga rikicin Isra’ila da Falasdinu, cewar rahoton Newsweek.

Kara karanta wannan
Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan
An ayyana kafuwar Israel a ranar 14 ga Mayu, 1948, amma sai a ranar 11 ga Mayu, 1949 ne Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a hukumance.
A lokacin, yawancin ƙasashe 58 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da ita, duk da wasu sharudda da aka gindaya kafin karɓar ta a matsayin cikakkiyar mamba.
Sai dai duk da wannan amincewa, ba duk ƙasashen duniya ba ne suka amince da Israel, inda zuwa shekarar 2023, ƙasashe 165 ne kawai daga cikin 193 suka yarda da ita.
Yawancin ƙasashen Larabawa da waɗanda Musulmi suka fi yawa na ci gaba da ƙin kulla cikakkiyar alaƙa da Isra'ila, suna mai danganta matsayinsu da rikicin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
1. Jamhuriyar Nijar - Ta yanke alaka da Isra'ila
Kasar Nijar na daga cikin kasashen farko da suka ki kulla alakar diflomasiyya da Israi'la tun a shekarar 2019 saboda rikici da Falasdinawa.
Daukar matakin ya biyo bayan mamaye titunan birnin Niamey da ya kasar suka yi saboda abin da ke faruwa a Falasdin, cewar Gulf News.
Hakan ya biyo bayan sabunta alaka da Isra'ila a 1996 bayan shafe shekaru 23 da yanke alakar saboda rikicin Gabas ta Tsakiya a 1973.

Kara karanta wannan
'Za mu ci gaba da kai hari,' Isra'ila ta sake tsokano Iran da ta kashe mutane a Lebanon

Source: Getty Images
2. Libya - Ba ta amince da Isra'ila ba
Libya wacce ke goyon bayan Falasɗinawa sosai ba ta amince da Isra'ila ba a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Wata ganawa da aka yi a Agustan 2023, ta haifar da zanga-zanga a ƙasar da mafi yawan al’ummarta Larabawa ne.
Ministan harkokin wajen Isra’ila, Eli Cohen, ya ce wannan “ganawa mai tarihi” ita ce “mataki na farko” wajen kafa dangantaka da Libya, cewar BBC.
Israel na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da ƙasashen Larabawa da waɗanda Musulmi suka fi yawa waɗanda har yanzu ba su amince da ita a hukumance ba.
Sai dai Majalisar Shugabancin Libya, wadda ke wakiltar yankuna uku na ƙasar, ta ce haramun ne a kulla alaƙa da Isra'ila.

Source: Getty Images
3. Tunisia - Ta yanke alaka da Isra'ila
A watan Oktoba na shekarar 2023, majalisar dokokin Tunisia ta gabatar da wani kudiri na doka da zai haramta duk wata hulɗa da Isra'ila.
Sai dai a ranar 2 ga Nuwamba, an dakatar da zaman kaɗa ƙuri’a kan kudirin, inda ya umurci ‘yan majalisar su yi watsi da shi, kamar yadda wani bayani daga Wikipedia ya ce.
Mohamed Ali, ɗan majalisa kuma mai kula da rahoton kwamitin ‘Yancin Dan Adam da ‘Yanci, ya yi iƙirarin cewa Amurka ta yi barazanar kakaba takunkumin tattalin arziki da na soja idan aka amince da kudirin.
A yayin yaƙin Gaza da ya fara a shekarar 2023, yawancin ‘yan Tunisia sun haɗa kai wajen goyon bayan dokokin hana alaƙa da Israel, sakamakon ƙin amincewa da Isra'ila da kuma ƙasashen Yamma.

Source: Getty Images
Sauran kasashen da ke takun-saka da Isra'ila
Sauran kasashen da suka yanke alaka da kuma kin amincewa da Isra'ila a matsayin kasa sun hada da:
4. Algeria
5. Comoros
6. Djibouti
7. Mali
8. Mauritania
9. Somalia
Kasashen Afirka da Isra'ila ta kai farmaki
A baya, mun kawo muku rahoton cewa yakin Iran da Isra’ila na ci gaba da tayar da hankali a duniya duba da asarar rayuka da dukiyoyin al'umma da ake yi.
Isra'ila ta taba kai hare-hare a wasu kasashen Afirka a tarihi, lamarin da ya shafi siyasa da tsaron yankin.
A wasu kasashen, an kai hare-haren sama kan masana’antu da ayarin makamai, yayin da a wasu aka gudanar da harin domin ceto fasinjoji.
Asali: Legit.ng
