Iran Ta Gano Karyar da Amurka Ta Sharara kan Mashigar Hormuz, Ta Fadi Gaskiya
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi karin haske kan ikirarin Amurka cewa jiragen ruwanta sun ratsa mashigar Hormuz
- Kasar ta bayyana cewa babu wani jirgin Amurka da ya bi ta yankin yayin da ake ci gaba da yarjejeniya tsakanin kasashen biyu
- Tashin hankalin ya ƙaru kan mashigar Hormuz yayin da Iran da Amurka ke musayar zarge-zarge masu karo da juna
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa kan rahotannin da ke cewa jiragen ruwan Amurka sun ratsa mashigar Hormuz.
Kasar ta karyata rahoton inda ta ce babu wani irin abu mai kama da haka da aka gani a yankin mai muhimmanci.

Source: Facebook
Kafafen yaɗa labarai na gwamnati sun ambato wani babban jami’in soja yana cewa babu wani jirgin Amurka da ya ketare mashigar, cewar Al Jazeera.
Majiyoyi a Iran suka ce hukumomi sun bayyana hakan ne yayin da suke ƙaryata rahotannin da aka fara yadawa daga wasu kafofin yada labaran kasashen waje.
Rahoton da aka yada kan mashigar Hormuz
Rahoton ya zo ne bayan wata kafar labarai ta Amurka ta bayyana cewa wasu jiragen ruwan sojin ƙasar sun ratsa yankin, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin ɓangarorin biyu, cewar New York Post.
Rundunar 'US Central Command' ta ce jiragen ruwan yaƙi guda biyu na Amurka sun ratsa mashigar Hormuz domin fara aikin cire nakiyoyin ruwa da Iran ta shimfiɗa.
“Yau mun fara aikin samar da wata sabuwar hanya, kuma nan ba da jimawa ba za mu sanar da wannan hanya mai aminci ga masana’antar jiragen ruwa domin ƙarfafa zirga-zirgar kasuwanci cikin ‘yanci."
- In ji kwamandan rundunar, Admiral Brad Cooper.
Tun da farko, Iran ta bayyana cewa ta gargadi jiragen ruwan yaƙin Amurka da kada su shiga mashigar, tare da barazanar kai musu hari idan suka yi kuskure.

Source: Getty Images
Abin da Trump ya ce ka mashigar Hormuz
Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma bayyana cewa sun fara aikin “tsabtace” mashigar, yana mai cewa an lalata ƙarfin sojin ruwa da na sama na Iran.
Sai dai hukumomin Iran sun yi watsi da wannan ikirari, suna mai cewa babu wani motsi na sojojin Amurka da ya faru a mashigar, tare da jaddada cewa rahotannin ba su da tushe.
Mashigar Hormuz na daga cikin wurare masu matuƙar muhimmanci a duniya, inda ake safarar mai, kuma tana ci gaba da zama wuri mai zafi a rikicin siyasa, cewar DW.com.
Mashigar Hormuz: Iran ta shirya jaza wa Amurka
Mun ba ku labarin cewa Majalisar dokokin Iran ta gabatar da sabon daftarin doka domin tsara yadda za a sarrafa mashigar Hormuz wanda ake ya magana a kai.
Shugaban kwamitin ayyuka, Rezaei Kochi, ya ce daftarin ya haɗa da sababbin ƙa’idoji kan zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tsarin karɓar kuɗin jangali.
Daftarin ya tanadi haramta wasu jirage, karɓar haraji da riyal, da kuma yadda za a raba kuɗaɗe don tsaro da walwalar al’umma.
Asali: Legit.ng

