Trump Ya Fadi Babbar Barazana 1 da har Yanzu Iran Take da Shi ga Kasashen Duniya

Trump Ya Fadi Babbar Barazana 1 da har Yanzu Iran Take da Shi ga Kasashen Duniya

  • Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta fara "share" abubuwan da ke kawo cikas a mashigar ruwan Hormuz domin amfanin duniya
  • Tattaunawa ta farko tsakanin Amurka da Iran ta kankama a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan ƙarƙashin jagorancin JD Vance da Mohammad Qalibaf
  • Shugaban kasar Amurka dai ya yi ikirarin cewa yanzu barazana daya ce Iran take da ita yayin da ya ce an riga an kashe shugabanninsu na da

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka – Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa dakarun sojojin Amurka sun fara aikin "share" mashigar ruwa ta Hormuz don ba jirage damar wucewa.

Trump ya yi wannan magana ne a daidai lokacin da aka buɗe tattaunawar zaman lafiya ta farko tsakanin jami’an Amurka da na Iran a Pakistan.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi babban matsalar Amurka a shirin yarjejeniyar zaman lafiya

Trump ya ce sun fara share nakiyoyin da Iran ta dasa a mashigar Hormuz.
Shugaban Amurka, Donald Trump, da mashigar ruwan Hormuz. Hoto: FADEL SENNA.
Source: Getty Images

Trump ya fadi barazanar da Iran take da shi

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya bayyana cewa wannan mataki "kyauta ce ga duniya," ciki har da ƙasashen China, Japan, Jamus, da sauransu.

Ya ƙara da cewa shugabannin Iran na da sun riga sun mutu, kuma dukkan jiragen ruwan Iran masu dasa nakiyoyi a tekun Hormuz yanzu haka suna ƙasan tekun.

Sai dai ya ce yanzu babbar barazanar da Iran take da shi ga kasashen duniya shi ne nakiyoyin da ta dasa a Hormuz, kuma ya ce ko a hakan ma, an nutsar da jiragensu.

A cikin sakon da ya wallafa, Trump ya ce:

“Shugabannin su da suka dade suna mulki yanzu duk ba sa tare da mu, godiya ga 'Allah.' Yanzu babbar barazanar da suke yi ita ce jirage za su iya nutsewa a teku idan suka yi karo da nakiyoyinsu, amma abin lura shi ne, yanzu haka jiragensu 28 da ke dasa nakiyoyin sun nutse a kasan tekun."

Kara karanta wannan

Bayan tsagaita wuta, Trump ya fadi aikin da Amurka za ta yi tare da Iran

An yi wa jirgin Amurka gargadi a Hormuz

Bayanan sa ido kan hanyoyin ruwa sun nuna cewa aƙalla jirgin yaƙin Amurka guda ɗaya, USS Michael Murphy, ya ratsa ta mashigar a yau Asabar, kamar yadda aka wallafa a shafin Maritime Traffic.

Wani babban jami’in sojan Iran ya yi iƙirarin cewa jirgin ya juya da baya bayan da aka yi masa gargaɗin za a kai masa hari, sai dai fadar White House ta ƙaryata wannan ikirari, inda ta tabbatar da cewa jiragen Amurka da dama sun ratsa mashigar ba tare da wata matsala ba.

An fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a Pakistan.
Babban allon sanarwa da ke nuna shirye shiryen tattaunawar Iran da Amurka a birnin Islamabad, Pakistan. Hoto: Farooq NAEEM / AFP via Getty Images
Source: Twitter

Tattaunawar Iran da Amurka a Islamabad

Wannan tattaunawa da ake yi a Islamabad, wadda ƙasar Pakistan ke jagoranta, ita ce yunƙuri mafi girma na kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe mako bakwai ana yi, wanda ya samo asali daga harin ba-zata da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, shi ne ke jagorantar tawagar Amurka, wadda ta haɗa da Jared Kushner da Steve Witkoff.

Kara karanta wannan

Ana murna an tsagaita wuta, Trump ya yi maganar da za ta iya harzuka Iran

A ɓangaren Iran kuma, Shugaban Majalisar Dokoki, Mohammad Qalibaf, da Ministan Harkokin Waje, Abbas Araghchi, ne ke wakiltar ƙasar.

Tawagar Iran ta isa birnin Islamabad, Pakistan

Tun da fari, mun ruwaito cewa, babbar tawagar jami’an ƙasar zuwa birnin Islamabad na ƙasar Pakistan domin fara tattauna war sulhu da Amurka yau Jumma'a, 10 ga Afrilu, 2026.

Wannan mataki na nuni da cewa Iran ce kasar farko da ta isa Islamabad, birnin zai zama babbar cibiyar diflomasiyya ta duniya a kwanaki masu zuwa.

Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ne zai jagoranci ɓangaren Amurka maimakon wakilai na musamman, kuma ana jiran isarsu Pakistan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com