Mojtaba: Halin da Sabon Jagoran Addini na Iran Yake ciki kan Lafiyarsa
- Hare-haren Amurka da Isra'ila sun raunata Mojtaba Khamenei a ranar farko ta yakin da aka fara a Gabas ta Tsakiya
- Wasu majiyoyi na kusa da shi sun bayyana kalar raunukan da ya samu a hare-haren wadanda suka yi silar rasuwarsa mahaifinsa
- Majiyoyin sun bayyana cewa duk da raunukan da ya samu, yana shiga cikin harkokin gudanar da mulki a Iran
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Sabon jagoran addini na ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei, yana ci gaba da murmurewa daga munanan raunuka da ya samu.
Mojtaba Khamenei yana murmurewa ne daga raunukan da ya samu a fuskarsa da kuma ƙafafunsa sakamakon harin sama da ya yi sanadin kisan mahaifinsa a farkon yaƙin.

Source: Getty Images
Tashar Reuters ta bayyana cewa mutane uku na kusa da shi suka shaida mata hakan a rahoton da ta fitar ranar Asabar, 11 ga watan Afrilun 2026.
Wadanne raunuka Mojtaba Khamenei ya samu?
Majiyoyi duka ukun sun bayyana cewa fuskar Khamenei ta samu rauni a harin da aka kai gidan jagoran da ke tsakiyar Tehran, sannan ya samu babban rauni a ƙafa ɗaya ko duka biyun.
Duk da haka, majiyoyin waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce jagoran mai shekaru 56 yana samun sauƙi kuma har yanzu tunaninsa yana nan garau.
Majiyoyi biyu daga ciki sun ƙara da cewa yana halartar tarurruka da manyan jami’ai ta hanyar sauraron sauti, sannan yana saka hannu wajen yanke manyan shawarwari da suka shafi yaƙin da kuma tattaunawa da Washington.
Bayanan da majiyoyin suka bayar su ne mafi bayani filla-filla game da yanayin jagoran a cikin makonni da dama.
Tashar ta bayyana cewa ba ta iya tabbatar da bayanan ba ta wata hanyar daban.

Source: Getty Images
Ba a san inda Khamenei yake ba
Har yanzu ana boye wurin da Khamenei yake, yanayin lafiyarsa, da ikon sa na gudanar da mulki, domin ba a fitar da hoto, bidiyo, ko muryarsa ba tun bayan harin da kuma naɗa shi a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa a ranar 8 ga Maris, 2026

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Ofishin jakadan Iran a majalisar dinkin duniya bai amsa tambayoyi ba kan girman raunukan Khamenei ba ko kuma dalilin da ya sa har yanzu ba a nuna hotonsa ko muryarsa ba.
Ayatollah Khamenei ya sha da kyar
An ji wa Khamenei rauni ne a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko na yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar, a harin da ya kashe mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei. Matar Mojtaba Khamenei, surikinsa, da matar ƙaninsa suna cikin danginsa da aka kashe a harin.
Duk da cewa babu wata sanarwa daga gwamnatin Iran kan girman raunukan nasa, wani mai karanta labarai a gidan talabijin na ƙasar ya bayyana shi a matsayin "Janbaz" kalmar da ake amfani da ita ga waɗanda suka ji raunuka sosai a yaƙi, jim kaɗan bayan naɗa shi jagora.
Tawagar Iran ta isa Pakistan
A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta isa Pakistan don tattaunawa da Amurka.
Tawagar za ta tattauna da takwarorinta na Amurka don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta kan yakin da ake yi.
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ke jagorantar tawagar wadda ta isa birnin Islamabad.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
