Iran Ta Faɗi Babban Matsalar Amurka a Shirin Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Iran Ta Faɗi Babban Matsalar Amurka a Shirin Yarjejeniyar Zaman Lafiya

  • Mataimakin shugaban ƙasa na farko na Iran, Mohammad Reza Aref ya yi magana kan yiwuwar gudanar da yarjejeniya
  • Aref ya ce sakamakon tattaunawar Islamabad zai dogara gaba ɗaya kan fifikon Amurka a tattaunawar zaman lafiya
  • Ya bayyana cewa yarjejeniya mai amfani ga ɓangarorin biyu na yiwuwa idan Amurka ta mai da hankali kan muradunta na fifita kanta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Mataimakin shugaban ƙasa na farko na Iran, Mohammad Reza Aref ya bayyana abin da zai kawo matsala a tattaunawa.

Aref ya bayyana cewa sakamakon tattaunawar da ke gudana a Islamabad zai dogara kacokan kan fifikon Amurka wanda zai iya jawo matsaloli.

Iran ta nuna fargaba kan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani saƙo da ya mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafin X a yau Asabar 11 ga watan Afrilun 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Sabon shirin yaki: Amurka ta fadi manyan makaman da ta zargi China za ta ba Iran

Yadda yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin Donald Trump.

An fara kai hari ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 a birnin Tehran wanda ya yi ajalin mutane da dama tare da barnata wurare masu muhimmanci a kasar.

Harin ya yi sanadin mutuwa marigayi tsohon jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro wanda ya sauya salon yaki baki daya.

Daga bisani, Iran ta yi martani mai zafi inda ta kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila da Amurka wanda ya jawo wa ƙasashen asara mai yawa.

Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka zai iya rushewa
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Iran ta nuna fargaba kan yarjejeniyar zaman lafiya

Aref ya ce akwai yiwuwar cimma yarjejeniya mai anfani ga kowa idan wakilan Amurka suka mayar da hankali kan muradunsu na “America First”.

Sai dai ya yi gargadi cewa duk wani sauyi zuwa tsarin “Isra'ila First” zai kawo cikas ga tattaunawar, inda ya ce hakan zai haifar da rashin cimma yarjejeniya gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan

Ya ƙara da cewa a irin wannan yanayi, Iran za ta ci gaba da kare kanta da ƙarfi fiye da da, tare da jaddada cewa hakan zai janyo ƙarin tsada ga duniya baki ɗaya.

Ya ce:

"Idan muka yi tattaunawa a Islamabad da wakilan da ke fifita “Amurka”, akwai yiwuwar cimma yarjejeniya mai anfani ga ɓangarorin biyu da ma duniya baki ɗaya.
" Amma idan muka fuskanci wakilan da ke fifita Isra'ila, ba za a cimma wata yarjejeniya ba; dole ne mu ci gaba da kare kanmu da ƙarfi fiye da da, kuma duniya za ta fuskanci ƙarin tsada."

Iran ta yi watsi da barazanar Trump

A baya, kun ba ku labarin cewa Kasar Iran ta yi watsi da barazanar Donald Trump bayan ya ba ta wa'adin awa 48 kan tattaunawa da yake neman a yi.

Iran ta kira hakan da rashin daidaito, tare da gargadin kai farmaki mai tsanani idan Trump ya aiwatar da abin da ya fada kamar yadda ya ke yawan yi mata barazana.

Janar Ali Abdollahi ya ce Iran za ta kai farmaki mai muni kan Amurka da Isra’ila idan aka lalata kayayyakin more rayuwa wanda ya jawo suka daga ƙasashen duniya da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.