Iran Ta Dauki Wani Mataki da Ya Sa Ta Shiga gaban Amurka a Shirin Zaman Sulhu a Pakistan

Iran Ta Dauki Wani Mataki da Ya Sa Ta Shiga gaban Amurka a Shirin Zaman Sulhu a Pakistan

  • Tawagar Iran mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisa Ghalibaf ta isa Islamabad domin tattaunawar sulhu da jami’an Amurka
  • Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ne zai jagoranci ɓangaren Amurka maimakon wakilai na musamman, kuma ana jiran isarsu Pakistan
  • Rahoto ya nuna cewa Amurka na so a kawo ƙarshen yaƙin domin daidaita farashin makamashi da rage hauhawar farashin kayayyaki a duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Pakistan – Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya tabbatar da isar babbar tawagar jami’an ƙasar zuwa birnin Islamabad na ƙasar Pakistan domin fara tattauna war sulhu da Amurka yau Jumma'a, 10 ga Afrilu, 2026.

Wannan mataki na nuni da cewa Iran ce kasar farko da ta isa Islamabad, birnin zai zama babbar cibiyar diflomasiyya ta duniya a kwanaki masu zuwa.

Tawagar Iran ta isa Pakistan don tattaunawar sulhu da Amurka
Babban allon sanarwa da ke nuna shirye shiryen tattaunawar Iran da Amurka a birnin Islamabad, Pakistan. Hoto: Farooq NAEEM / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Sulhu da Amurka: Tawar Iran ta isa Pakistan

Kara karanta wannan

Ministan Pakistan ya yi kaca kaca da Isra'ila kan zubar da jini a duniya

Tawagar Iran ta haɗa da ƙwararru a fannoni daban-daban, waɗanda aka bayyana a matsayin mutanen da za su yi tattaunawa mai tsauri kan sharuɗɗan da Iran ta gindaya, in ji rahoton The Guardian.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan, karkashin ministan harkokin wajen kasar, Ishaq Dar, ta tabbatar da karɓar baƙuncin tawagar a yau.

Tawagar ta ƙunshi manyan jiga-jigan gwamnatin Iran, ciki har da:

  • Mohammad Bagher Ghalibaf - Shugaban majalisar dokokin Iran.
  • Abbas Araghchi - Ministan harkokin waje.
  • Ali Akbar Ahmadian - Shugaban majalisar tsaro ta kasa.
  • Abdolnaser Hemmati - Gwamnan babban bankin Iran.
  • Mohammad Bagher Zolghadr - Tsohon kwamandan dakarun IRGC.

Har yanzu dai babu tabbas ko za a ci gaba da tattaunawar ne daga inda aka tsaya a Geneva, ko kuma za a fara sabon lissafi ne baki ɗaya.

Tasirin tattaunawar Iran da Amurka ga Trump

Rahoton Aljazeera ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump tana matuƙar son ganin an kawo ƙarshen wannan yaƙi cikin gaggawa.

Wannan ya biyo bayan matsin lamba na siyasa da yake fuskanta, da kuma buƙatar daidaita farashin man fetur da makamashi da ya tashi a faɗin duniya.

Kara karanta wannan

Yaƙi bai ƙare ba: Iran ta ƙaddamar da sababbin hare hare kan Saudiyya da ƙasashe 3

Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, shi ne zai jagoranci tattaunawar a madadin Amurka yau. Masana na ganin cewa naɗa Vance maimakon wakilai na musamman na nuna cewa fadar White House ta ɗauki batun da matuƙar muhimmanci.

Tawagar Iran ta isa Islamabad, Pakistan don tattauna wa da Amurka.
Tawagar Iran da ta kunshi shugaban majalisa, Mohammad-Bagher Ghalibaf da ministan harkokin waje, Abbas Araghchi lokacin da suka isa Islamabad. Hoto: @TheSaviour
Source: Twitter

Amurka na kau da kai daga bukatun Iran

Duk da isar tawagar ta Iran, akwai alamun cewa Amurka na ƙoƙarin kau da kai daga wasu buƙatun na Iran kafin a zauna yau.

Iran dai na neman tabbacin tsaro da kuma dage takunkumai, yayin da Amurka ke son ganin an daina barazanar da ke shafar hanyoyin makamashi na duniya.

A kwanaki masu zuwa ne za a iya tantance ko wannan zama zai samar da maslaha mai ɗorewa ko kuma za a ci gaba da samun takun-saƙa tsakanin manyan ƙasashen biyu.

JD Vance ya fallasa shirin Amurka kan Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya kama hanyar zuwa birnin Islamabad domin halartar zaman tattaunawa da kasar Iran.

Kafin jirginsa ya tashi daga birnin Washington, JD Vance ya bayyana shirin Amurka da fatan da take a zaman tattaunawar da za ta yi da Iran.

Sai dai, mataimakin shugaban kasar, ya yi gargadi cewa idan Iran ta yi kokarin yaudarar Amurka a tattaunawar, ba za su yi mata sassauci ba ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com