Tun kafin Gama Sulhu da Iran, Shugaban Amurka na Shirin Ballo Yakin da Zai Jefa Kasashe a Bala'i
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin ci gaba da yakar Iran idan tattaunawar sulhu ta gaza
- Trump ya yi wannan barazana ne yayin da ake shirye-shiryen tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad
- Ana ganin dai wannan magana da shugaba Trump ya yi na nuna cewa kasashen duniya za su sake fsukantar matsala idan sulhu bai yiwu ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi barazanar komawa fagen daga da kasar Iran matukar tattaunawar sulhu da za a fara a Pakistan ba ta yi nasara ba.
Barazanar Trump na zuwa ne yayin da tawagar Amurka da ta kasar Musulunci ta Iran suka nufi birnin Islamabad na Pakistan domin tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa yayin da hankula suka koma kan wannan tattaunawa, Shugaba Trump ya yi barazanar ci gaba da kai hare-hare kan kasar Iran.
Trump ya barazanar kai hari Iran
Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na sake loda sababbin makamai a jiragen ruwanta na yaki domin kai hari kan Iran idan tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Pakistan ta gaza.
A wata hira da jaridar New York Post, Trump ya ce:
“Muna yin wani sabon shiri, muna sake shirya jiragen ruwa da mafi kyawun makamai da aka taba kerawa, sun fi wadanda muka yi amfani da su a baya,”
“Idan ba mu cimma yarjejeniya ba, za mu yi amfani da su, kuma za mu yi amfani da su yadda ya kamata.”
Shugaban Amurka ya haifar da rudani
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, Trump ya yi amfani da kalmomi masu jan hankali inda ya rubuta, "sake saiti mafi karfi a duniya,"

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka
Wannan sako ya kara jefa damuwa game da yiwuwar sabon matakin soji da shugaban na Amurka ka iya dauka idan tattaunawar sulhu ba ta kai ga nasara ba.

Source: Getty Images
Shirin fara tattaunawa ya yi nisa
A gefe guda kuma, Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya nufi birnin Islamabad domin jagorantar tawagar Amurka a tattaunawar karshen mako da Iran.
Haka zalika, Iran ta tabbatar da cewa wakkilata za su isa birnin Islamabad a daren jiya Alhamis, lamarin da ake kallo a matsayin matakin da zai kawo karshen yakin da aka shafe fiye fa wata guda ana yi.
Amma maganganun da Trump ya yi game da shirin sake kai hari sun kara jefa tantama kan abin da ka iya zuwa ya dawo ba a cimma matsaya a wannan tattaunawa ba.
Iran ta gindaya sharadin zama da Amurka
A baya, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin Iran, Mohmmad Bagher Ghalibaf, ya yi magana kan tattaunawa da Amurka don samar da zaman lafiya mai dorewa.
Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa ba za a fara tattaunawa ba har sai an tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila ke kai wa Lebanon.
A cewarsa, dakatar da kai hare-hare na cikin sharuddan da dole a cika su kafin lasar Iran ta amince a fara tattaunar sulhu da Amurka a Islamabad.
Asali: Legit.ng
